Saturday, October 3, 2015

Iftila’in Hajjin Shekarar 2015 da na Sauran Wasu Shekarun

30 Ga Satumba, 2015

Daga: Amir Abdulazeez

F
aruwar haɗarurruka  masu kawo asarar rayuka da jin raunuka a aikin Hajji ba wani  baƙon abu ba ne, amma  tun bayan da adadin yawan mutanen duniya ya haura biliyan 3 tsakanin shekarun 1960 zuwa 1970, sai ya kasance faruwar irin waɗannan haɗarurruka ta ƙara yawaita kuma a duk lokacin da suka faru a kan yi asarar rayuka masu yawa tare da jikkatar alhazai da dama. Yawan mutanen duniya na ƙaruwa, yawan Musulmi na ƙaruwa sannan kuma yawan mahajatta na ƙaruwa. Yanzu haka yawan Musulman duniya ya haura a biliyan 1.6 kuma a dukkan shekara kusan Musulmai miliyan 2 zuwa 3 ne suke zuwa Saudiyya domin sauke faralli.
Daga shekarar 1975 zuwa shekarar 2015 da muke ciki, alƙaluman hukumomin Saudi Arabia sun nuna cewar sama da mutane 4,841 ne suka rasa ransu a dalilin haɗarurruka daban-daban, yayin da wasu dubannai suka samu raunuka. Duk waɗannan alƙaluma basu shafi alhazai waɗanda suke mutuwa ɗai ɗai ko nan da can a dalilin wata rashin lafiya ba. Mafi yawan waɗannan haɗarurruka dai basa wuce turmutsutsu a yayin jifan sheɗan. A cikin muhimman haɗarurrukan da suka wakana a aiyukan aikin Hajji a tsawon shekaru 40, 8 ne daga ciki kawai basu da  alaƙa da turmutsustsu domin sun faru ne a dalilin gobara, ruguzau, zanga-zanga da dai sauransu.

Haɗarurrukan Aikin Hajji a Shekaru 40
Duk da cewar abu ne mai wahala a iya tantance tarihin tun lokacin da irin waɗannan muhimman haɗarruka masu tasiri suka fara faruwa a aikin Hajji, to amma abu ne sananne cewar a duk lokacin da a kan yi wani abu wanda yake tara dubunnai ko miliyoyin jama’a, to dole ne baza a fitar da tsammanni yiwuwar faruwar haɗari, tsautsayi ko jarrabawa daga Ubangiji ba. A mafi yawan lokuta, rundunar dubunnan mahajjata masu tattaki daga wani waje zuwa wani wajen ta kan kawo turmutsutsu wanda ya kan kawo asarar rayuka da jikkata mutane da dama.
A ranar 2 ga watan Julin 1990, turmutsutsu a hanyar wucewar alhazai ta Ma’aisim wacce take fita daga Makkah zuwa Mina da kuma filin Arafah ya yi sanadiyyar mutuwar alhazai 1,426, da yawa daga cikinsu ‘yan ƙasashen Malaysia, Indonesia da Pakistan.  Wannan shi ne haɗari mafi muni a cikin shekaru 40. Turmutsutsu ya yi sanadiyyar rasa alhazai da yawa da kuma jikkkata wasu da dama a shekarun 1994, 1998, 2001, 2003, 2004, 2006 da kuma 2015.
A  ranar 15 ga Afrilun,1997, gobara a tantunan mahajjata, ta yi sanadiyyar mutuwar alhazai 343 da raunata 1,500. Yanzu sababbin tantuna na zamani da ake yi wa alhazai amfani dasu, an sana’antasu ta yadda wuta ba ta iya ƙona su. Haka kuma a shekarun 1975 da 2011, gobara ta kawo asarar rayuka da jikkata wasu da dama a aikin hajji.
A ranar 11 ga Julin, 1991, haɗarin jirgin saman Nigerian Airways mai lamba 2120 wanda ya taso daga Jeddah zuwa Sokoto, ya yi sanadiyyar mutuwar dukkan alhazai 247 ‘yan Najeriya da kuma ma’aikatan jirgin 14. Jirgin ya faɗi ne  jim kaɗan bayan tashi daga  Filin Jirgin Saman Sarki Abdulaziz. Haka ma haɗarurrukan jiragen sama sun afku a hanyar zuwa ko dawowa daga aikin hajji a tsakanin ƙasashen duniya daban-daban a shekarun 1973, 1974, 1978, 1979 da 1980 inda kusan dukkan alhazan da abun ya shafa suka rasa rayukansu.
Rugujewar otal ɗin Al-Gaza a kusa da Harami a 2006 ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 76 da raunata 64. Sannan faɗowar ƙugiya a cikin Harami a ranar 11 ga Satumbar 2015 ya kashe mutane 118 tare da raunata 394.
An rasa alhazai da yawa sakamakon ɓarkewar cututtuka da annoba a shekarun da suka gabata. Kafin fara aiyukan Hajjin 2006, alhazai 243 ne suka rasu daga ƙasashe daban-daban sakamakon cututtuka masu alaƙa da zuciya, gajiya, tsufa da kuma rashin lafiyar da aka zo da ita tun daga gida. A shekarun baya cututtuka irinsu zazzaɓi, kwalara, polio, mura da ƙyanda sun yi sanadiyyar rasuwar wasu tsirarun alhazai.

Jifan Sheɗan (rami-aljamarat)
Jifan sheɗan wanda a ke gudanar da shi a birnin Mina, yana daga cikin rukunan aiyukan Hajji mafi haɗari a shekarun baya  saboda yawan jama’a, musamman a lokacin da mutanen suke tsallaka gadar jamarat wacce take sada su zuwa ga inda za su yi jifan. Mafi yawan cinkoso, turmutsutsu da asarar rayuka ya kan auku ne  a wajen jifan sheɗan.

Jamarat

Bayan turmutsutsun shekarar 2004, Gwamnatin Saudiyya ta yi aikace-aikace masu yawa a wajen gadar jamarat. An ƙara yawan hanyoyi da wajen tsallakawar mutane da kuma hanyoyin fita na ko-ta-kwana. Bayan haka kuma an musanya manyan durakun nan guda uku masu wakiltar Sheɗan ɗin da wani shafaffen bango babba na kankare domin gujewa turereniyar da alahazai suke yi a ƙoƙarin samun guri saitin waɗannan duraku a shekarun baya.
Bayan wani turmutsutsun a shekarar 2006, Gwamnatin Saudiya ta ƙara yin wasu rushe-rushe, sauye-sauye, faɗaɗe- faɗaɗe da gyare-gyare a jamarat domin sauƙaƙa wa alhazai yayin jifan sheɗan. Sannan kuma an ɓullo da tsaruka domin hana cinkoso da kuma shiga haɗari. To amma duk da wannan matakai, an sake samun turmutsutsu a wannan waje a shekarar 2015 da muke ciki.

Haɗarurrukan Aikin Hajjin Bana na Shekarar 2015
A baya bayannan, in banda shekarar 1990, babu wata shekara da aka samu rashin rayukan alhazai kamar a wannan shekara da muke ciki. Tun da farko dai, kamar kowacce shekara, an samu mutuwar alhazai ɗaiɗaiku daga ƙasashe daban-daban sakamakon dalilai na rsahin lafiya da kuma ajali. Bayan haka kuma faɗowar ƙugiya a cikin Masallacin Harami a ranar 11 ga Satumbar 2015 ya kashe mutane 118 tare da raunata 394. Tuni dai Gwamnatin Saudiyya ta tabbatar da biyan diyyar Riyal miliyan guda guda ga iyalan mamata da kuma waɗanda suka samu nakasata din-din-din a haɗarin wannan ƙugiya. Sannan kuma waɗanda suka samu raunuka aa basu Riyal 500,000. Bayan haka an yi alƙawarin kujerun aikin Hajjin baɗi biyu ga iyalan kowanne mamaci tare da sanyasu a cikin baƙin Sarkin Makka na musamman.


Ranar 24 ga Satumbar 2015, hukumomin Saudi Arabia sun bayyana mutuwar sama da alhazai 769 da raunatar sama da 860 a wajen jifan sheɗan. A baya bayannan masu sanya idanu daga ƙasashe daban-daban sun fitar da sanarwar cewar adadin waɗanda suka rasu daga wannan turmutsutsu kuma aka ga gawarwakinsu ya kai 1,090 yayin da kuma har yanzu ake neman alhazai da dama waɗanda ba a gani ba. Wannan haɗari ya faru ne yayin da rukunin wasu alhazai masu dawowa izuwa masaukinsu bayan sun yi jifa, suka biyo hanyar tafiya a maimakon su bi ta hanyar da aka ware domin masu komowa inda suka haɗu kuma suka yamutsa da alhazai masu tafiya izuwa jamrat.

Asarar Rayukan Alhazan Najeriya a Hajjin 2015
Duk da dai cewar har yanzu ba a gama tattara yawan alhazan Najeriya da suka rasu ko suka ji ciwo a wannan aikin Hajji na bana ba, amma a ranar Juma’ar da ta gabata shugaban hukumar alhazai ta ƙasa, Alhaji Abdullahi Mukhtar ya bayyana adadin alhazan Najeriya da suka mutu a wajen turmutsutsun jamrat kaɗai a matsayin guda 74 yayin da sama da 71 suka samu raunuka yayin da yawan alhazan da ba again ba ya kai 244. Alhazan da suka rasu sun fito daga jihohin Bauchi, Borno, Cross-Rivers, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi da Nassarawa. Waɗanda suka ɓace kuma sun fito daga jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Ekiti, Abuja, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kwara, Nassarawa, Ondo, Niger, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara. Wannan ya biyo bayan alhazai 6 da suka rasu yayin da 4 suka ɓata a faɗowar ƙugiyar cikin Masallacin Harami yayin kuma da wasu ƙarin 20 suka mutu tun da farko bisa dalilai na rashin lafiya ko kuma ajali.
Yanzu haka dai Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga Hukumar Aikin Hajji ta ƙasa da ta gaggauta bin ba’asin duk wani alhajin Najeriya da ya rasu, ya ji rauni ko kuma ya ɓata domin sanar da ‘yan uwansa halin da yake ciki.
 
Yawan Alhazan Duniya a duk shekara
Tun daga lokacin da jiragen sama suka zama ruwan dare a duniya, kullum yawan maniyyata aikin Hajji yake ƙaruwa daga ƙasashe daban-daban. Wannan ya biyo bayan samuwar sauƙin sufuri saɓanin a shekaru masu yawa a baya da ake zuwa a a motoci, jiragen ruwa, a kan dabbobi, wasu ma har a ƙasa.
A cikin shekaru goma da suka gabata, ƙasar Saudiyya tace ta karɓi baƙuncin yawan alhazai miliyan 25 sannan kuma kamfanin dillacin labarai na Reuters ya rawaito cewar a cikin waɗannan shekaru goma, shekarar 2012 ita ta fi kowacce shekara yawan alhazai da adadin mahajatta miliyan 3.16 yayin da shekarar 2013 ta fi kowacce ƙarancin mahajatta da alhazai miliyan 1.98. A mafi yawan shekaru, alhazan ƙasar Indonesia su kan fin na ko’ina yawa inda suke kasancewa kimanin 20% na yawan alhazan da ba ‘yan ƙasar Saudiyya ba a kowanne aikin Hajji.

                                                                                                              
Tasirin Rashin Jituwar ƙasashen Saudi Arabia da Iran ga Aikin Hajji
Babu shakka, dukkan mai nazari a kan al’amuran yau da kullum, zai ga cewar akwai rashin jituwa a tsakanin ƙasar Saudi Arabia da kuma ƙasar Iran. Wannan rashin jituwa kuwa tana nema ta ci gaba da kawo matsaloli a a cikin aiyukan Hajji. Yayin da ƙasar Saudiyya take zargin alhazan Iran da ɓullo da matsaloli da gangan domin kawo cikas ga aikin Hajji, ita kuwa Iran ta na zargin Saudia Arabia da gazawa wajen samar da cikakken tsaro a aikin Hajji.
A ranar 31 ga Julin 1987, mutane 400 ne suka mutu yayin da dubannai suka jikkata a lokacin da jami’an tsaron Saudiyya suka yi arangama da wasu mahajjatan Iran masu zanga-zanga. Ko shakka babu wannan abu ne mara daɗi wanda za a iya gujewa afkuwarsa. Ya kamata ƙasashen biyu su yi ƙoƙari su samu daidaito  a tsakaninsu ta yadda saɓani da rashin jituwarsu a siyasance ba zai dinga shafar aikin Hajji ba.
Ko a wannan iftila’in da ya faru na Hajjin bana, an samu taƙaddama tsakanin Saudia da Iran a kan silar afkuwar matsalar da kuma adadin alhazan da suka mutu. Ita dai Iran ta zargi Saudia da ƙin bayyana ainihin adadin yawan waɗanda suka rasu inda take ganin yawansu ya haura a 4,000, kodayake ba ta bayar da wata hujja gamsasshiya ba a kan wannan adadi. Ita dai Iran, ita ce ƙasar da ta fi kowacce ƙasa rasa rayukan alhazai a Hajjin wannan shekara inda sama da mahajjatanta 400 ne suka rasu.

Ta Yaya Za a Kori Gaba?
Ko shakka babu, mahukuntan ƙasar Saudiyya suna iya bakin ƙoƙarin su domin hana afkuwar haɗurra a yayin aikin Hajji, to amma duk da wannan ƙoƙari har yanzu idan tsautsayi ya gifta a kan samu asarar ɗumbin rayuka da jikkatar jama’a. Ya kamata su ƙara ƙoƙari a kan ƙoƙari, kada su gajiya. Babu wani abu da za a iya yi wanda ya wuce rigakafi.
Idan muka kalli mafi yawan haɗarurraka kuma sai muga cewar masu alaƙa da cinkoso ne. Mataki na farko da ya kamata a a ɗauka shi na a duba yiwuwar taƙaita yawan mahajjatan da suke fitowa daga kowacce ƙasa a duk shekara. A duba, a tantance a gani, duk wanda ya taɓa zuwa aikin Hajji sau biyu ko sau uku, to a dakatar da shi daga zuwa aikin sai bayan wasu shekaru domin sauƙaƙa cinkoso. Maimakon mahajatta miliyan 2 zuwa 3 da ƙasar Saudiyya ta ke karɓa kowacce shekara, a rage su zuwa miliyan 1 ko 1.5. wannan zai kawo sauƙin cinkoso ƙwarai da gaske.
Sannan kuma su mahajattan su kansu, su ƙara zage damtse wajen gujewa matakai da zasu kawo cikas. Kowacce ƙasa ta dinga yin bita tare da ilmantar da alhazai ba wai kawai yadda za su yi ibadar Hajji ba kaɗai, har da yadda za su gujewa haɗurra da kuma matakan da zasu ɗauka na gaggawa idan haɗarin ya auku.
Bayan haka, ƙasashen Musulmi su ɗauka cewar samun nasarar aikin Hajji ya rataya a wuyayensu ne baki ɗaya ba wai a wuyan ƙasar Saudiyya kawai ba. Ita ma Saudi Arabiar, a fahimtar da ita hakan. A taru a samar da wani kwamiti mai wakilcin dukkan ƙasashe domin gudu tare a tsira tare. Kada a ce za a taƙaita ikon Saudiyya da hukumominta, wajen tsarin aikin Hajji, amma ya zama sauran ƙasashe su zamo masu ruwa da tsaki wajen tsare-tsaren cikin fahimta da manufa mai kyau.
Allah Ubangiji Ya karɓi shahadar waɗanda suka rasu, marasa lafiya kuma, Allah Ya basu lafiya.

©Mujallar Mikiya, 2015.

A KULA: An ciro mafi yawan bayanan dake cikin wannan sharhi daga shafin Wikipedia, daga kamfanin dillacin labaran ƙasar Faransa na AFP, wallafe-wallafen hukumomin kula da aikin Hajji na ƙasar Saudi Arabia, kafafen yaɗa labarai na ciki da wajen Najeriya da kuma ta wasu hanyoyi masu yawa wanda yawansu ba zai bayar da dama a bayyanasu ba.

Shafin Mallam Amir a Twitter shine: @AmirAbdulazeez  
   


Sunday, September 6, 2015

SHARHI: Mecece Makomar ƙananan Hukumomin Najeriya?

3 Ga Satumba, 2015

 
Daga: Amir Abdulazeez

T
arihin ƙananan hukumomi a ƙasarnan ya samo asali ne tun kusan daga lokacin da Turawan Ingila suka haɗa gundumar Arewaci da Kudancin Najeriya domin samar da ƙasa ɗaya. Tun a wancan lokaci Turawa suka samar da shiyyoyin mulkin mallaka a ƙarkashin tsarin mulki wanda ba na kai tsaye ba na Native Authorities wanda ya bai wa sarakuna damar yin mulki mai taƙaitaccen iko ga yankunansu kafin daga baya a tsame sarakunan su kansu daga mulkin kacokam. Gwamnatoci daban-daban sun sha yi wa tsare-tsaren ƙananan hukumomi gyare-gyare da kwaskawarima tare da ƙarawa da rage adadin yawansu har sau tara daga 1914 zuwa 1999. Tasrin ƙananan hukumomi kamar yadda muka sansu a yanzu ya samu ne daga sauye-sauyen da aka gudanar a shekarun 1976, 1979, 1984, 1988, 1989 da 1999.

Duk da cewar gwawnatocin jihohi daban-daban sun yi yunƙure-yunƙure daga shekarar 2000 zuwa 2007 na ganin sun ƙara yawan ƙananan hukumomi a jihohinsu, har yanzu dai adadin yawan ƙananan hukumomi guda 774 ne kamar yadda ya ke a Kundin Tsarin Mulkin ƙasa na shekarar 1999. To amma kuma akwai jihohin da bayan ƙananan hukumomin su, sun ƙirƙiri ƙananan  gundumomin mulki da samar da ci gaba masu kama da ƙananan hukumomin. Misali, Jihar Lagos ta na da ƙananan hukumomi 22 amma ta na da irin waɗannan gundumomi waɗanda ita take samar musu da kuɗaɗen gudanarwa har guda 37. Akwai irin waɗannan gundumimi a jihohin Yarabawa sosai.

Fahimtar kusan kowa ita ce an ƙirƙiri ƙananan hukumomi domin matso da gwamnati kusa da talaka. Bayan haka, akwai ƙayadaddun aiyuka da Kundin Tsarin Mulkin ƙasa na 1999 ya tanadar musu. Muhimman aiyukan sune bayar da shawarwari da za su inganta tattalin arziƙin gwamnatin jiha; samar da maƙabartu da gidajen kula da marasa galihu; bayar da lasisin kekuna, kwale-kwale da kurar turawa ta ɗaukar kaya; kafawa tare da gudanar da mayanku, kasuwanni, tashoshin mota da gidajen wanka; gina ƙananan  tituna, layuka, saka fitlun kan titi da fitar da magudanar ruwa; bai wa tittuna da layuka sunaye da yi wa gidaje lamba; kwashe shara da kwatoci; yin rajistar haihuwa da ta mutuwa. Bayan haka an sanya ƙananan hukumomi  su zamo masu taimaka wa gwamnatocin jihohi wajen bayar da ilimin firamare, ilimin manya da ilimin koyon sana’o’i; bunƙasa noma da kuma yin dukkan wasu aiyuka da Majilusun Dokokin Jihohi suka kallafa musu.

Sai dai kuma duk da waɗannan ɗinbin aiyuka da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora wa ƙananan hukumomi, kuma bai basu damar cin cikakken gashin kansu ba. A ƙarƙashin sashe na II, ƙananan  sassan 7(1), (2) da (3), Kundin Tsarin  Mulkin ya nuna cewar gwamnatocin jihohi su zasu samar da dokokin da zasu tabbatar da wanzuwa, tsari, aiyuka da kuma kashe kuɗaɗen waɗannan ƙananan hukumomi. Wannnan ya nuna cewa rayuwarsu kusan kacokam ta na hannun jihohi. Wannan kusan ita ce a yanzu babbar matsalar da take damun ƙananan hukumomi.

Kafin dawowar dimokraɗiyya a 1999 har zuwa farkon dawowar ta, a kan ji ɗuriyar ƙananan hukumomi suna ɗan taɓuka aiyukan raya ƙasa duk da cewa akwai manyan matsaloli da suke fama da su tun a wancan lokaci. Amma yanzu kusan gwamnatocin jihohi sun kalmashe su, ba ma a jin ɗuriyarsu, a wasu jihohin ma kamar babu su.

Babbar matsala ta farko da take damun ƙananan hukumomi a yanzu ita ce ta tsarin zaɓar shugabanninsu. Tun bayan shekarar 1999 inda aka gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin Najeriya bai ɗaya, har yanzu ba a samu ingantattun zaɓuka a mafi yawan ƙananan hukumomi ba. Duk jam’iyyar da take mulki a wata jihar, ta kan tabbatar da cewa ta lalata tsarin zaɓen ta yadda za ta cinye 100% na zaɓukan ciyamomi da kansiloli. Gwamnoni su kan yi amfani da hukumomin zaɓen jihohi wajen shirya gurɓatattun zaɓuka a ƙananan hukumomi wanda dama tun farko dalilai na siyasa ba sa bari a samar da ingantattun ‘yan takara tun da farko. Wasu jihohin ba ma sa yin zaɓen kwata-kwata sai sun ga dama, sai dai gwamnoni su naɗa kantomomi. A Jihar Anambra an taɓa kwashe shekaru 13 daga 2002 har zuwa 2014 ba a yi zaɓukan ƙananan hukumomi ba. Wata ƙarin matsalar kuma ta wannan fuskar ita ce, Majalisun Dokoin Jihohi da dokar ƙasa ta bai wa alhakin kula da ƙananan hukumomin tare da basu kariya sun zuba ido sun kasa kataɓus yayin da gwamnoni suke ta cin karensu ba babbaka a kan ƙananan hukumomi.

Babbar matsala ta biyu da take damun ƙananan hukumomi ita ce rashin basu kuɗaɗensu da gwamnoni suke yi. Kusan yanzu ya zama ruwan dare a kowacce jiha, idan kuɗin ƙananan hukumomi sun zo daga Gwamnatin Tarayya, sai jihohi su danne su hanasu ko kuma su tsakurar musu abin da suka ga dama da sunan asusun haɗin gwuiwa. A tsarin kason arziƙin ƙasa, ƙananan hukumomi su suke da kaso 21%, jihohi na da 30%, ita kuwa Gwamnatin Tarayya take da 49%.  Misali, bayanan da Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta wallafa a shafukan jaridun ƙasarnan cikin satattakin da suka gabata sun nuna cewar an rarraba kuɗaɗe masu yawan Naira Biliyan N923,881,185,187.63 a tsakanin gwamnatocin ƙasa a watan Yunin 2015 waɗanda aka fitar da bayanansu a ƙarshen watan Julin 2015. A wannan kasafi, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira Biliyan 419.3, Gwamnatocin Jihohi 36  sun samu Naira Biliyan 254.3, Gwamnatocin ƙananan hukumomi 774 sun samu Naira Biliyan 179.6. To amma kason  ƙananan hukumomi ya na shiga ne ta asusunsu na haɗin gwuiwa da jihohi, wanda kuma a mafi yawan lokuta jihohin  ba sa basu. A wasu lokutan wasu jihohin masu ɗan adalci su kan hanasu kuɗaɗen amma sai su yi musu aiyuka da kuɗin, yayin da wasu kuwa su kan hanasu kuɗin da aikin bakiɗaya, sai su ɗebi kuɗin su yi aikin jiha da su, duk da cewar su ma jihohin suna da nasu kason daga Gwamnatin Tarayya.

Wannan ya haifar wa da ƙananan hukumomi rauni ba kaɗan ba da kuma shiga wani yanayi na rashin tabbas da rashin makoma. Saboda rashin kuɗi, ƙananan hukumomi ba sa iya gudanar da mafi yawan aiyukan da aka ɗora musu su aiwatar.

Babbar matasala ta uku da take damun ƙananan hukumomi itace almundahana da cuta. Bahaushe kan ce wai idan ɓera da sata, to daddawa ita ma da wari. Shugabanni da ma’aikatan ƙananan hukumomin Najeriya sun yi ƙaurin suna wajen tafka almundahana da kuɗaɗen al’umma.  A lokutan da jihohin suka sakar musu kuɗaɗensu, sai a nemi aiyukan da suka yi da kuɗin a rasa, maimakon haka sai dai a ga ciyamomi da kansiloli da manyan ma’aikatan ƙananan hukumomi suna wadaƙa da kuɗaɗe, suna gina manyan gidaje tare da yin buƙatun da ko yaro ƙarami ya san sun fi ƙarfin albashi da alawus-alawus ɗinsu. Wata matsalar ta su ƙananan hukumomin kuwa ita ce ta sakaci da wasa da aiki. Sai ka ziyarci ma’aikatun ƙananan hukumomi sau shurin masaƙi a ranakun aiki amma ba za ka tarar da mafi yawan ma’aikata ba. Shi kansa ciyaman da kansiloli ba sa zuwa sai sun ga dama. A mafi yawan lokuta ba sa zuwa sai ƙarshen wata lokacin da aka turo kuɗi.

Yanzu dai ƙananan hukumomi a Najeriya sun zamo ƙadangaren bakin tulu, a kashesu a kar tulu, a bar su, su ɓata ruwa. Idan aka ce za a soke su, to tabbas za a raba talaka da gwamnati mafi kusa da shi kuma mahukunta za su ƙara yin nesa da talaka. Komai lalacewarsu dai, akwai amfanin da suke yi wa talaka na ƙasa. Bayan haka ‘yan ƙananan aiyuka masu amfanar unguwanni da garuruwa da ƙananan hukumomin su kan yi duk za a yi asararsu domin ba zai yiwu gwamnatocin jihohi da ta tarayya su samu damar shiga kowanne lungu da saƙo ba.

Idan kuma aka ce za a bar ƙananan hukumomi su ci gaba da wanzuwa, to fa waɗancan matsaloli ba za a rabu da su ba, wataƙila ma sai dai in ba ayi wasa ba su ci gaba da ƙaruwa. Tarin kuɗaɗen da ake turowa ƙananan hukumomi domin amfanin talaka za su cigaba da zurarewa a banza da hofi. A shekarar 2003, Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin Cif Olusegun Obasanjo ta kafa wani kwamiti da zai yi nazari a kan makomar ƙananan hukumomi, amma sai ‘yan Najeriya su ka ƙi bai wa yunƙurin goyon baya domin a zaton su Obasanjo kawai so ya ke ya ruguje ƙananan hukumomin domin Gwamnatin tarayya ta dinga riƙe kasonsu.

Abu na farko da ya kamata a yi domin magance waɗannan matasloli, shi ne Gwamnatin Tarayya ta gaggauta kafa wani kwamiti makamancin irin na Obasanjo, wanda zai ƙunshi wakilan ta da na Fadar Shugaban ƙasa, wakilan ƙungiyar gwamnonin Najeriya NGF, wakilan ƙungiyar Kakakan majalisun dokokin jihohi ta ƙasa, wakilan ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta ALGON, wakilan majalisun dattawa da ta tarayya ta ƙasa, wakilan ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta NULGE, wakilan ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC  da kuma wakilan ƙungiyoyin kare manufofin ci gaba domin lalubo bakin zaren wannan matsaloli. Bayan nan majalisun dattawa da na tarayya sai su yi wa Kundin Tsarin Mulkin ƙasa gyara domin ya dace da ƙudurce-ƙudurcen da aka cimma a wancan kwamiti na farfaɗo da ƙananan hukumomi.

Kafin nan kuma kamata ya yi gwamnonin jihohi su yi wa kansu faɗa, su dubi Allah, su dubi talaka, su dinga bai wa ƙananan hukumomi  haƙƙoƙinsu kuma su ƙyalesu su yi aikinsu, su kuma a nasu ɓangaren, ciyamomi, kansiloli da ma’aikatan ƙananan hukumomi su yi wa Allah su gyara halayensu.

Shafin Mallam Amir a Twitter shine: @AmirAbdulazeez  

Abubuwa 10 da Muka Fahimta daga Gwamnatin Ganduje a Cikin Kwanaki 100

1 Ga Satumba, 2015

 
Daga: Amir Abdulazeez
 
A
n zaɓi Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Gwamnan Jihar Kano da gagarumin rinjayen yawan ƙuri’un da ba a taɓa ganinsu ba a tarihin Jihar Kano. Bayan haka kuma shi ne Mataimakin Gwamna na farko da ya taɓa zama zaɓaɓɓen gwamna  a tarihin siyasar Kano. Kusan kowanne ɗan takara ya kan samu mulkin Kano ne ta sanadiyyar abu ɗaya zuwa biyu amma Dakta Ganduje ya ɗare kan mulki bisa dalilai masu yawa. Farko dai ya samu mulki a bisa cancantarsa ta karan kansa da gogewarsa ta fuskar aikin gwamnati da kuma siyasa tare da fifikon da ya ke da shi ta fuskar ƙwarewa a kan sauran ‘yan takara. Na biyu an zaɓe shi gwamna a dalilin ƙarfi da farin jinin jam’iyyarsa haɗe kuma da yayin ta da ake yi sannan kuma da rashin farin jinin ragowar jam’iyyun da suka kara da ta sa jam’iyyar. Abu na uku, an zaɓe shi saboda ƙarfin guguwar Shugaba Buhari wacce ta yi awon gaba da duk wani abu da ya tsaya a kan hanyar ta. Abu na huɗu, an zaɓe shi saboda ƙarfin gwamnati da ya ke hannunsu tare da kuma da farin jinin maigidansa tsohon gwamna Kwankwaso. Waɗannan sune manyan dalilan da suka kawo Ganduje kan mulki.
Alhamdulillah, kwanci tashi yanzu gwamnatin Ganduje ta kwana 100 a kan mulki kuma ko shakka babu mutanen Kano suna da tulin bure-bure da ƙudurce-ƙudurce a kan wannan gwamnati saboda irin gagarumar gudunmawar da suka ba ta. Kodayake kwanaki 100 sun yi kaɗan a iya yi wa gwamnati mai wa’adin shekaru huɗu wani cikakken alƙalanci, amma sun isa a gane inda gwamnatin da kuma waɗanda suke jagorancin ta suka dosa tare da hasashen me za ta yi ko me za ta iya iya yi, menene ba za ta iya yi ba, musamman idan aka yi la’akari da wasu abubuwan da suka faru kai tsaye daga gwamnatin ko kuma daga wasu abubuwa da suka shafe ta ko da ba kai tsaye ba. A cikin kwanaki 100 na Ganduje, mun fahimci abubuwa da yawa, to amma ga guda 10 daga cikinsu;
Ganduje ya Fara Nuna ƙwarewa a Aikin Gwamnati kuma zai Tafi da Matasa;
Muhimmin aikin da Ganduje ya fara yi shine na rage yawan ma’aikatun Jihar Kano daga ashirin da wani abu zauwa 14 kacal inda ya harhaɗe wasu ma’aikatu da wasu domin ingantuwar aiki da kuma guje wa taci-barkatai a aikin gwamnati.
Idan kuma aka yi la’akari da naɗe-naɗen muƙaman da Gwamna Ganduje ya gudanar a cikin kwanakinsa 100, to za mu iya cewa matasa ne za su juya akalar gwamnatin Jihar Kano a shekaru huɗu masu zuwa. Duk kuwa inda aka ce an sa matasa a gaba, to za a ga aiki ba kasala da jan ƙafa in dai matasan masu kishi ne ba lalatattu ba. Sai dai kawai matsalar ita ce, ba a san ko gwamnan zai sakar wa matasan da ya naɗa mara su yi fitsari ba ko kuma kawai ya yi musu naɗin jeka-na-yi-ka ne a matsayin tukwuicin goyon bayansu lokacin yaƙin neman zaɓe. Wani lokaci kuma su matasan su kan yi ƙorafin ba a basu dama, amma kuma daga an basu sai su ƙasa bai wa maraɗa kunya. Ko ma dai menene, zuba matasa a a cikin gwamnati abu ne mai kyau da ya ke nuna an ɗauko hanyar ci gaba, sai dai kuma muna fata kada matasan da aka naɗa su juye su koma matatsa.
 
Har Yanzu Sabon Liman bai Wartsake daga Zama Na’ibi ba;
Duk da cewar Ganduje ya yi kwanaki 100 a matsayin cikakken liman a maimakon na’ibi da ya shafe shekaru takwas ya na yi, alamu sun nuna kamar har yanzu bai wartsake daga na’ibintaka ba.
Wasu masharhanta siyasa da harkokin mulki suna ganin har yanzu bai yi kama da gwamna mai cikakken iko ba, tamkar tsohon gwamna Kwankwaso ya na tasiri sosai a kan yadda ake gudanar da gwamnati kuma kamar shi tsohon gwamnan ya yi masa dabaibayi. Rahotannin cikin gida sun nuna cewar akwai shawarwari masu kyau da ƙudurce-ƙudurce da makusantansa  da kuma ‘yan kwamitin karɓar mulkinsa suka bashi kuma ya nuna ya karɓa, amma a cikin kwanaki 100 babu wasu alamun cewa zai yi aiki da su saboda tsoron zai baƙanta wa Kwankwaso ko kuma za su iya canza alƙiblar gwamnatinsa daga ta Kwankwasiyya. Kodayake dai shi kansa gwamna ya faɗa tun da farko cewar yadda ɗillin ta kan yi ɗillin, haka kaza ta kan yi ƙwan nan, sai dai fa ba duka ƙwai ne ya kan yi kaza ba, wani ƙwan ya kan yi gunya.
Har Yanzu Majalisar Dokokin Kano ‘Yar Amshin Shata ce;
Majalisar Dokoin Jihar Kano, kamar dukkan sauran Majalisun Dokokin Jihohin Najeriya, ta kasance a mafi yawan lokuta ‘yar amshin shatar ɓangaren zartarwa. Tun daga yanayi mai kama da ɗauki-ɗora da aka bi wajen fitar da shugabancin Majalisar Dokokin ta Kano, ta bayyana a fili cewar ba lallai su iya taka wa gwamnati birki ba yayin da ta kauce hanya. Jama’ar Kano sun ɗauka za ta ɗan yi wasu tambayoyi dangane da wasu abubuwa da suka faru  a kwanakin baya kamar misalin dakatar da ma’aikatan shara sama da guda 2000 da gwamnati ta yi daga aiki da kuma hargitsi da ya taso a hukumar KAROTA, amma sai aka ji shiru. Kai a taƙaice ma da wahala a iya nuna wani abu da majalisar ta yi na karan kan ta ba wai wanda gwamna ya tura mata ba a cikin kwanaki 100 ɗin da suka gabata. Ko wannan ya na da alaƙa da cewar dukkan ‘yan majalisu 40 ɗin ‘yan jam’iyyar APC ne mai mulki ba tare da ɗan adawa ko ɗaya ba ko kuma alamu ne na ‘kyakkyawar’ alaƙa da ɓangaren zartarwa, ba mu sani ba. Kwanannan dai Gwamnatin Kano ta ware wa kowacce mazaɓar ɗan majalisa Naira Miliyan 50 domin yin aiyukan mazaɓu. Da alama dai ‘yan amshin Shata sun fara jin daɗin waƙar Shatan.
 
An Kashe Ofishin Fes Ledi a Kano;
Gwamna Ganduje dai za a iya cewa ya ɗora a kan inda Sanata Kwankwaso ya tsaya a yunƙurin tsame matan gwamnoni daga sha’anin mulki a bayyane. A fili dai babu wanda zai ce ya ji ɗuriyar matar Kwankwaso ko Ganduje a sha’anin mulkin Kano daga 2011 zuwa 2015. Wannan ya sha ban-ban daga abin da ya ke faruwa a lokacin tsohon Gwamna Shekarau. To amma sai dai wani abin tambaya a nan shi ne, menene laifi don matar mai mulki ta shigo cikin sha’anin mukin mijin ta da kyawawan tsare-tsare domin taimaka masa a gina ƙasa da al’umma? Wasu na ganin babu laifi idan hakan ba zai  kawo wawure dukiyar al’umma da sunan ofishin ‘First Lady’ ba. Wasu kuwa suna ganin tunda akwai Ma’aikatanun Ci gaban Mata a matakin tarayya da kuma dukkkan jihohi waɗanda suke da ma’aikatan gwamnati birjik da kwamishinoni, to babu buƙatar sai matan masu mulki sun shigo gwamnati.
Ko ma dai menene, ba za a taɓa iya raba matar mai mulki da tsoma baki a cikin mulkin sa ba, ko dai a fili ko kuma a ɓoye. Wani lokacin ma gara ta tsoma a filin, don a ɓoyen  ba a san abin da za ta angiza mijin ya yi ba.
Ganduje Sai Ya Fi Shekarau Haɗa Siyasa da Addini;
Da wahala  a samu wani gwamna a Kano da ya yi amfani da addini wajen saye zukatan jama’a ba kamar tsohon gwamna Mallam Shekarau.  A tsawon mulkinsa na shekaru takwas, kodayaushe maganar Shekarau ita ce siyasarsa addininsa kuma addininsa siyasarsa. Za mu iya cewa Shekarau ya ci ribar wannan tsari ko kuma aƙida ta sa duk da ya ke kuma a ƙarshe tsarin ko aƙidar ta sa ta saka shi a cikin tsaka-mai-wuya a siyasance.
Idan muka yi la’akari da yadda Khadimul-Islam Shiekh Ganduje da magoya bayansa suke addinantar da gwamnatinsa da siyasarsa a cikin kwanaki 100 da suka gabata, to za mu iya cewa zai dame Shekarau ya shanye nan da wani lokaci kaɗan, wataƙila ma kafin wasu kwanaki 100 ɗin masu zuwa.
 Kwankwaso Ya Bar Baya da ƙura ;
Kwankwaso ya ɗebi ma’aikata da yawa, ya ciyar da ‘yan makarantar firamare abinci kyauta, ya tura ɗalibai ƙasahen duniya domin ƙaro ilimi kyauta, amma kuma ya tafi ya bar basussuka da kwantan aiyuka na kusan Naira Biliyan 400 kamar yadda Kwamitin Karɓar Mulki na Ganduje ya bayyana. Wato dai ba mu san me ya kamata mu yi ba idan mun tuna da Kwankwaso, dariya, kuka ko kuma duka biyun? Kodayake gwamna Ganduje ya fito kafafen yaɗa labarai yace waɗannan  basussuka ba laifi ba ne tunda tsabar aiki ne ya sa aka same su, to amma  a cikin kwanaki 100 da suka wuce har yanzu ba a ga wani tsari da ya bayyana ba a fili ƙarara wanda ya ke nuna yadda za a biya waɗannan basussuka kuma zuwa wane lokaci?
Bayan haka, idan aka raba aiyukan Kwankwaso gida uku, kusan sama da kashi ɗaya bai ƙarasa su ba, duk da cewa wasu ma ya dinga ƙaddamar da su a hakan ba a gama ba, sannan kuma a cikin kwanaki 100 da suka wuce babu wani daga cikin kwantan aiyukan da aka ƙarasa balle a ƙaddamar. Wasu aiyukan ma tun da Kwankwason ya tafi  ba a sake ganin ƙeyar ma’aikata ko ‘yan kwangilar a gun aikin ba. Duk wannan ma mai sauƙi ne a kan aiyukan da ake ikirarin cewar ƙarasasu za a yi, bayan a gaskiyance ma kusan ko farasu ma ba a yi ba. Idan da mai tantama, to ya ziyarci  titunan kilomita biyar biyar  da ake yi musamman a ƙananan hukumomin ƙauyuka.
 
Ƙananan Hukumomi basu Farfado ba Har Yanzu;
A halin yanzu, za mu iya cewa  ƙananan hukumomin Jihar Kano a mace suke murus domin akwai ƙananan hukumomin da aka rawaito cewar shugabanninsu suna yin wata guda basu  ziyarce su ba balle kuma sauran  ma’aikata.  Shekaru huɗu gwamnatin Kwankwaso ta yi ta na hana ƙananan  hukumomi cikakkun kuɗaɗensu, shi kuwa mulki ba ya yiwuwa sai da kuɗi.
Majiyoyi masu tushe sun nuna cewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka bai wa Ganduje gagarumin goyon baya a tsakanin shugabannin ƙananan  hukumomi shine ko dai alƙawarin da ake cewa ya yi musu na zai dinga  basu kuɗaɗensu ko kuma kyakkywan zaton da suke masa  na cewar ba zai riƙe musu haƙƙoƙin ƙananan hukumominsu ba.
A cikin kwanaki 100 da mulkin Ganduje, har yanzu kusan ƙananan  hukumomi suna nan yadda suke, ba-cas-ba-as. Kodayake an ce har yanzu ciyamomi suna ta duban hanya dangane da batun kuɗaɗen nasu, amma sun manta cewar Ganduje shi ne kwamishinan ƙananan hukumomi a shekaru huɗun da Kwankwaso ya yi ya na hanasu kuɗaɗensu.
 Tsafta Ita ce Bakandamiyar Ganduje;
Bayan rantsar da Gwamna Ganduje, sai da aka shafe kwanaki 7 cur ana kwashe shara a Kano. Bayan nan kuma gwamnatin ta ɓullo da tsarin tsafatace ma’aikatun gwamnati a duk juma’ar ƙarshen wata tare da ware ƙarin Ranar Lahadin ƙarshen wata don yin wata ƙarin tsaftar amma ba tare da an hana zirga-zirga ba. Wannan na nuna cewar  gwamnatin a tsaye ta ke  kyam a kan tsafta wanda kuma zai taimaka wajen inganta kiwon lafiya. Kowacce gwamnati ta na da bakandamiya, me yiwuwa idan aka ci gaba a haka, tsaftar muhalli zai zamo abin da za a dinga tuna gwamnatin Ganduje da shi bayan ta tafi.
Wani hanzari ba gudu ba shi ne, duk da wannan ƙoƙari na gwamnati, har yanzu ba a raba tituna da unguwannin Birnin Kano da shara. Shin mutane ne suke amfani da damar cewa gwamnati na kwashe sharar shi ya sa suke zubar da ita ko’ina ko kuwa irin abin nan ne  da ake cewa idan dambu ya yi yawa, ba ya jin mai?
Ganduje da Kwankwaso za su ɓata amma ba Yanzu ba;
Masana mulki sun tabbatar da cewa ba a yin sarki biyu a gari ɗaya. Sannan kuma ma’abota sharhi kan harkar siyasa suna ganin cewa mai mulki ba zai taɓa samun nasara sosai ba sai ya zamo mutumin kansa wanda kuma hakan na nufin ya ɓata da iyayen gidansa.
A 1999, Kwankwaso ya ɓata da iyayen gidansa irinsu Rimi, Musa Gwadabe, Gwadabe Satatima da Hamisu Musa. A 2003, Shekarau ya ɓata da su Janar Magashi, AVM Mukhtar, Naja’atu da su Danzago. Don haka abu ne mai wahala Ganduje ba su ɓata da Kwankwaso ba in dai ba sun matuƙar kai zuciya nesa ba wanda da wahala masu kai komo a tsakani su bari a kai zuciya nesan.
A tsawon kwanaki 100 da suka gabata, wasu  ‘yan siyasa suna ta kai gwauro suna kai mari a kan lallai sai sun haɗa Ganduje da Kwankwaso faɗa. Kwankwaso ya binne abubuwa da yawa wanda dole sai an tono su za a samu zaman lafiya, idan kuma Ganduje ya shirya barin su a binne, to ya shirya wa rungumar abin da zai biyo ba tsakaninsa da mutanen Kano. Idan kuma zai tono su, to ɓatawa da Kwankwaso ta zama dole. Ganduje mutum ne dattijo mai juriya da haƙuri kuma ya daɗe ya na haƙuri da Kwankwaso, kodayke shi ma Kwankwason ya yi haƙuri da shi, amma fa yanzu ba lallai shi sabon gwamna ya iya ci gaba da yin haƙurin da ya yi a baya ba. Saboda haka masu kai gwauro suna kai mari, me kuke ci na baka ya na zuba?
Ganduje Ya Samu Damar Kafa Tarihi;
Idan da Kano za ta samu gwamna wanda zai tsakuro halayen Kwankwaso kaɗan, ya tsakuro na Shekarau kaɗan ya haɗa waje ɗaya, to da an yi lafiyayen gwamna. Misali a samu gwamna gogagge, mai ilimi, nutsuwa, tausayi da jin shawara kamar Shekarau kuma ya zamo jajirtacce, ma’aikaci, mara tsoro, mai cika magana kamar Kwankwaso.
Ganduje ya samu kansa a cikin wani yanayi mai cike da damar kafa tarihi. Kwankwaso da Shekarau sun mulki Kano shekaru takwas-takwas, duk an ga kamun ludayinsu. Ya na da damar ya kalli alkhairansu ya yi koyi sannan kuma ya kalli kura-kuransu ya kauce musu. A kwanakinsa 100 da ya yi a kan mulki, alamu sun nuna kamar abin da ya ya ke ƙoƙarin yi kenan, kodayake yanzu ya yi wuri a iya yin alƙalanci.
Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, bincike ya tabbatar da cewa mutum ba ya iya zama mai kishiyoyin hali biyu lokaci ɗaya, sai dai ya zama mai zafi ko mai sanyi, mai laushi ko mai tauri. Da Ganduje ya zama kamar Shekarau, da ya zama kamar Kwankwaso wanne ya fi?
Shafin Mallam Amir a Twitter shine: @AmirAbdulazeez  

Tuesday, June 16, 2015

SHARHI: Ta Yaya Za a Gyara Ilimi A Najeriya?

Daga: Amir Abdulazeez

A

n jima ana tattaunawa tare da yin yunƙuri akan batun farfaɗo tare da inganta ilimi a Najeriya, amma kusan babu wani abu bayyananne a ƙasa wanda ya ke nuna cewar an samu nasara ko kuma ana kan hanyar samun nasarar. Wataƙila wani ya tambaya, me ya sa za a farfaɗo da ilimi; shin a wane hali ya ke? Duk abin da ake zancen farfaɗo da shi, to ana  nufin a wani lokaci can a baya, ya na da ƙarfinsa da kuma kuzarinsa, amma a yanzu ya yi rauni. Haƙiƙa shekaru  kamar 30 zuwa sama baya, ilimin boko a Najeriya ya na da inganci ƙwarai da gaske; duk fannin da aka ce mutum ya karanta, to ba a wata tantama akan ƙwarewarsa a wannan fannin ko da kuwa shi ya fi kowa rashin mai da hankali a ajinsu. Wanda yak e da cikakkiyar shaidar gama makarantar sakandiri, ya fi mai karatun digiri a yanzu ilimi. Babu wanda ya ke tsoron tura ‘ya’yansa makarantar gwamnati domin ya na da tabbacin cewar zai samu ingantaccen ilimi. Amma a yanzu in dai ilimi mai inganci a ke so, sai dai makarantar kuɗi.

Idan muka duba tarihin shugabanni da manya-manyan masu faɗa-a-ji na ƙasarnan, sai mu ga cewar makarantar gwamnati ya yi kuma dukkan wani ilimi da wata ƙwarewa da ya ke taƙama da ita, to wancan ilimi shi ne tushensa. Abin da ya ke faruwa a wannan zamanin shi ne, ilimin ya na ƙara yawaita, amma ingancinsa ya na ƙara lalacewa. A wancan lokacin, ilimin ya na da ƙarancin yawa sakamakon rashin yawan jama’a da kuma rashin rungumarsa da al’umma ba su yi ba sosai, don haka ilimin boko sai wane da wane, to amma kuma ya na da matukar inganci.

Mafi yawancin makarantun kudi ba su haura shekarau 30 zuwa 35 da kafuwa ba, ma’ana an kafasu daga shekarar 1975 zuwa sama. Ko a wancan lokaci, ba wai an yi su ba ne saboda rashin ingancin ilimi a makrantun gwamnati, a’a ; an yi su ne saboda neman kuɗi da kuma ƙarancin makarantun su kansu. Yanzu kuwa, kusan babu inda  ake samun ilimi mai inganci sai a makarantun kuɗi masu zaman kansu. Makarantar gwamnati ta zama larura, babu wanda yak e son ta sai dole, ba don komai sai don cewar ba a bayar da wani ilimin kirki a cikinsu. A kan samu yara sun gama firamare amma ba za su iya rubuta ko da sunansu ba, haka za su tafi sakandire su gama, ba su san komai ba.

Muhimmancin ilimi ga rayuwar Ɗan Adam abu ne kusan da ba zai iya misaltuwa ko kwatantuwa ba. A dukkan abin da mutum zai yi dole sai ilimi ya shigo ciki; tun daga kan zaman rayuwar shi kansa, addini, sana’a har izuwa mu’amala da zamantakewa. Wannan ta sa dole ne a tsaya a gyara shi kuma a inganta shi domin samun kyakkyawar makoma.

Matsalar da aka sha fama da ita a baya shine gudun ilimi da ake yi musamman a Arewacin Najeriya, to amma yanzu wannan matsalar ta kau domin mafi  yawan mutane a yanzu sun koma makaranta kuma ba sa wasa wajen saka ‘ya’yansu a makaranta. Dawowar mulkin siyasa a shekarar 1999 ta bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen wannan. Mutane kusan kowa ba ya son a bar shi a baya kuma ya na so a dama da shi ko dai a cikin siyasa ko gwamnati ko a wani abu mai alaƙa da ita. Wannan ita ta sa yawan masu neman ilimi ya dinga ƙaruwa tun daga shekarar 2000 har zuwa yanzu a Najeriya. To amma ingancin ilimin kuma fa; baya ya ke ci ko gaba?

Idan muka ɗauki tsarin ilimi  a Najeriya tun daga matakin firamare har zuwa jami’a, sai mu ga cewa akwai matsaloli masu tarin yawa da suka dabaibaye shi. Matsalolin sun haɗa da rashin ingantattun malamai, rashin kyautatwa ma’aikatan ilimin, rashin kishin ilimin, rashin kyawun guraren ɗaukar ilimin, rashin kayan aiki  tare kuma da rashin aiki da shi kansa ilimin. Kodayake gwamnatoci a matakin tarayya, jihohi da ƙananan  hukumomi sun taka rawar gani a shekraun baya musamman daga 1999 zuwa 2003 wajen ganin ta samar da kyakkyawan yanayin karatu ta hanyar gine-ginen da gyare-gyaren ajujuwa, to amma har yanzu hakan bai wadatar ba domin yawan mutanen da suke buƙatar karatun ya ninninka ƙoƙarin da gwamnati ta ke yi wajen samar da shi da kuma inganta shi.

Duk ma ba waɗannan matsalolin da suke zayyane a sama ne babbar mishkila ba, babbar matsalar ita ce kullum ingancin ilimin baya ya ke yi kuma gwamnati ta kasa samo bakin zaren yadda za ta gyara al’amarin. Abin kuma ƙara dagulewa ya ke duba da cewa kullum mutanen Najeriya ƙara yawa suke yi, kuma masu buƙatar ilimin ƙara ninninkawa suke yi. Wani batun kuma shi ne abubuwa sun yi wa gwamnati yawa sosai kuma kullum kuɗaɗen shigar ta ko dai ƙara baya suke yi ko kuma darajar su ƙara faɗuwa ta ke yi saboda matsalar hauhawar farashi.

Duba da wannan, akwai buƙatar gwamnati ta ɗauki hanya mai sauƙi kuma nagartacciya wajen ganin ta ceto ilimi a ƙasaranan. Masu iya magana na cewa: ‘in duka ya yi yawa, na ka ake karewa’. Ko da ba zai yiwu a bi dukkan matakan inganta ilimi a Najeriya ba, to ya kamata a bi wasu daga cikin hanyoyin. Hanyoyin kuwa sun haɗa da inganta harkar malanta da koyarwa, bai wa ilimin martaba da daraja shi, sannan da tabbatar da cewa ana aiki da ilimin.

Babban mataki da gwamnati za ta ɗauka, shi ne ta bai wa kula da malamai fifiko akan komai. Wajibi ne gwamnati ta tabbatar cewa sai malamin da ya ke da cikakken ilimi da ƙwarewa ne kaɗai zai koyar a dukkan matakai. Bayan haka ta tabbatar ta na ɗaukar nauyin malaman lokaci bayan lokaci domin ƙaro karatu da yin kwasa-kwasai waɗanda za su ƙara musu ƙwarewa da sanin makamar aiki. Ban da wannnan, ya zama lallai ta ɗauki isassun malaman ta yadda aiki ba zai dinga yi wa malami yawa ba. Wato ya kasance malami bai fi ya shiga aji sau biyu ko uku a rana ba domin samun sararin yin bincike-bincike da sauran abubuwa masu alaƙa da kula da ɗalibai da kuma inganta iliminsa, sannan kuma ya kasance malami ya na koyar da ɗalibai kamar 30 zuwa 40 a lokaci ɗaya ta yadda zai iya kula da su gabaɗaya kuma ya nazarci yanayin ganewarsu da fahimtarsu amma ba ya saka ɗalibai sama da 100 a gabansa ba. Bayan haka, a samar da kyakkyawan albashi da alawus-alawus ga malaman makaranta, idan da hali ma ya kasance su suka fi kowa kyawaun albashi a cikin ma’aikatan ƙasa. Wannan zai  sa a dinga alfahari da sana’ar koyarwa  a maimakon a ƙyamace ta. Bayan duka wannan kuma sai a samar da wani tsari na sanya ido a kan malamai tare da yin tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama ya na wasa da aikinsa. Idan a ka yi wa malamai haka, to ko ba a gyara ajujuwa ba, ilimi zai farfaɗo domin sai da malami za a samu makaranta amma makaranta ba za ta samu ba in ba malami. Saboda haka gara a gyara malami a ƙyale makaranta a maimakon a ƙyale malami a gyara makaranta. Mutanen da a baya wasu ma a ƙarƙashin bishiya suka dinga karatu, amma saboda akwai ingantattun malamai, sai suka sami ilimi mai inganci.

Wani abu da gwamnati ya kamata kuma ta kiyaye shi ne muhimmancin ilimi daga tushe. Ya kamata gwamnatoci su fi mayar da hankula kan ilimin firamare fiye da na sakandire da na jami’a. Alamu sun nuna kamar cewa gwamnati, musamman ta tarayya ta fi damuwa da jami’o’i, ta fi yin aikace-aikace tare da kula da malaman jami’a fiye da sauran. Kuskuren a nan shine, ana ɗora gini ne  akan fandisho mara kyau da inganci. Ilimin firamare shi ne fandisho. Maimakon kafa jami’o’i barkatai waɗanda su kan lashe maƙudan kuɗaɗe wajen kula da su, kamata ya yi a koma a inganta ilimin firamare, domin mafi yawa tun a can suke baro ilimin.

Wata muhimmiyar matsala da ilimi ya ke fuskanta a Najeriya, ita ce ɗaukar sa da aka yi a matsayin hanyar neman abinci kaɗai. Misali kusan kowa ya na yin ilimin boko ne saboda ya gama ya karɓi takardar shaida domin ya samu aiki. Wannan ita ta kawo koma baya da cikas akan ainihin ginshiƙi da manufar yin ilimin shi kansa. Asali dai ilimi ana yin sa ne domin a koyi yadda za a sarrafa rayuwar Ɗan Adam, to amma yayin da aka ƙasƙantar da shi ya koma hanyar neman sana’a kaɗai, to dole a bi dukkan hanyoyi marasa kyau da nagarta domin ganin an same shi tunda buƙatar kawai ita ce a kawo shaidar karatu domin a ɗauki mutum aiki. Wannan ta sa manufar ilimi ta asali ta samu mummunar tawaya.

Wani ƙarin naƙasu kuma shi ne, shi kansa ɗaukar aikin, ba a yin sa dai-dai da irin ilimin da mutum ya karanta. Alfarma ta yi yawa a cikinsa, misali mutum zai karanta ilimin tarihi, amma sai ya ɓige da aikin banki, ko ya karanci ilimin fasahar injiniyanci amma sai ya ƙarke da aiki a matasyin sakatare mai sarrafa takardu.  Idan da akwai wani tasri da zai dinga tabbatar da cewa kowa abin da ya karanta, shi zai aikata, to wataƙila kowa zai mayar da hankali sosai a makaranta wajen ganin ya ƙware akan fannin ilimin da ya ke karanta gudun ka da ya ji kunya a wajen sharar fagen ɗaukar aiki ko a wajen gudanar da aikin kansa.

Abu na ƙarshe da ya kamata mu kula da shi shi ne, mu guji ɗaukaka takardar shaidar samun ilimi fiye ma da ilimin shi kansa. Wannan kuskure ne ba ƙarami ba. A zamanin yanzu sai ka ga mutum ya na da ilimin, amma saboda ba shi da shaidar ilimin sai a ƙasƙantar da shi akan wanda ya ke da takardar shaidar ilimin amma ba shi da ilimin a kansa. Wannan ita ta sa ake ta rububin samun takardar shaidar ilimi a maimakon ilimin. Zai yi kyau a dinga gwada ilimin mutum a aikace fiye da akan takarda domin wannan za ta sa kowa ya shiga taitayinsa a makaranta wajen ganin ya tsaya ya samu ingantaccen ilimi.

Ya zama wajibi a kan mu, da mu da gwamnati, mu taru mu ceto ilimi daga durƙushewa a Najeriya.