An bawa Bataye lambar yabo
.
✍️ Abdul gaffar isah
An karrama mashawarci na musanman ga shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa SA Abdullahi Ishaq Bataye da lambar girmamawa.
Hakan na zuwa ne kwana 2 bayan taron da aka gudanar na ɗaliban lafiya wanda akayi a Dawakin Tofa model primary.
An bawa Bataye lambar yabo tare da naɗa shi Jagoran ƙungiyar wadda Muhammad lawan Musa yake jagoranta.
A jawabin da yayi bayan bashi wannan ƙyauta ya godewa kafatanin ƴan ƙungiyar, sannan ya shawarci ƴaƴan kungiyar dasu haɗa kan su, ya kuma ƙara da cewa " Haɗa kai ne ze bada damar samun cigaba me ɗorewa a wannan ƙungiya, kazalika yace " Babu wani alheri daga Gwamnati daze tsallake ƙungiyar matuƙar suna da haɗin kai"
A ƙarshe ya shawarci ƙungiyar data yi koyi da abinda ƙungiyar NYSC tayi na gudanar da tsaftace muhalli a Dawakin Tofa wato (sanateshin)
No comments:
Post a Comment