Atiku Abubakar ya taya tawagar Tamaula ta mata murnar samun tagulla.
✍️ Abdul gaffar isah
Ɗan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya taya tawagar Flamingoes murnar samun tagulla, a gasar cin kofin duniya na mata.
A wani saƙo daya wallafa a shafin sa na facebook ya bayyana cewar " Ina taya Flamingoes din mu murnar samun lambar tagulla a gasar cin kofin duniya na mata na ƴan ƙasa da 17 a Indiya.
Ya kuma bayyana cewa " Fiye da mako guda da suka gabata, sun sami cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta mata ta ƴan ƙasa da 17 a karon farko. Yau kuma sun kawo mana lambar yabo.
A ƙarshe Atiku ya bayyana matuƙar jin daɗin sa da wannan lambar yabo da suka samu.
No comments:
Post a Comment