Saturday, October 15, 2022

 Yan Najeriya sun samu dubbunan kudade.


✍️ Saifullahi Abdulhamid Shu'aibu


A jiya ne yan Najeriya da dama suka samu dubban kudade ta lalitar bankanansu.


Mun samu labarin irin dubbunan kudade da yan Najeriya suka samu ta lalitar bankunansu, sai dai bamu rahoton musbbabin abin da ya sa ake tura kudaden ba amma dai shaidu da dama sun tabbatar da samun wannan kudi.


Wani shaidar gani da ido ya tabbatar mana da cewa mafi akasari anfi turawa mutane naira dubu hurhudu kai wasu ma har dubu sha biyar.


Badamasi Aminu wanda aka fi sani da Bass Alkanawui daya ne daga cikin wakilan Muryar Dawakin Tofa ya shaida mana cewa shima yau ya samu sakon dubu hudu ta bankinsa kuma yana tsammanin irin wannan kudaden ne da ake turawa yan Najeriyar se dai ya shaida cewa yana tsammanin kudaden daga babban bankin kasa CBN a turance ake tura kudaden.


Zamu cigaba da bibiyar labarin domin kara gano wadanda suka samu nasu sakonnin.


Friday, October 14, 2022

A yau ake bikin ranar Matuƙa Adai-daita sahu.


 A yau ake bikin ranar Matuƙa Adai-daita sahu.

✍️ Abdul gaffar isah

Ƙungiyar matuƙa babura masu ƙafa uku sun gadanarda bikin ranar Matuƙa Adai-daita sahu.

Ajiya ne wasu daga cikin mambobin ƙungiyar suka shedawa manema labarai cewa zasu gudanar da bikin ne ayau Juma'a.

Matukan sun bayyana cewa " Ayau juma'a zasu ɗauki ɗalibai kyauta, idan kuma sun ga wanda yake da buƙatar temako zasu shima zasu ɗauke shi kyauta ko kuma suyi masa ragi.

A jawabin da shugaban matukan yayiwa gidan Rediyo Nasara yace " Dubban matasa ne ke samun Arziki da sana'ar, sedai yace "kashi 95 cikin 100 matasa ne. Ya kuma bayyana hakan a matsayin babban cigaba.

Kotu ta yanke wa budurwa hukuncin wata 6 a gidan yari bisa laifin yin sojan-gona.

 Kotu ta yanke wa budurwa hukuncin wata 6 a gidan yari bisa laifin yin sojan-gona



Kotun Majistre 54 da ke unguwar Noman's Land a jihar Kano ta yanke wa wata matshiya, Zainab Salisu Sheka hukuncin watanni shida a gidan yari bisa laifin yin sojan-gona.


Tun da fari, ƴan sanda ne su ka gurfanar da Zainab a gaban kotun, ƙarƙashin Mai Shari'a Ibrahim Mansur, bisa amfani da kayan ƴan sanda ta na bada hannu a danjar kan titin New Road da ke Sabongari.


Lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara,  Barista Aminu Kawu ya roki kotu da ta karanto wa wacce ake tuhuma laifukan ta. Sai jami'in kotu Muhammad Zakirai ya karanto mata kuma ta amsa laifinta.


Sai dai kuma ta shaida wa kotun cewa aikin ne ya ke bata sha'awa shi ya sa ta yi.


Da ya ke yanke hukuncin, alkali Mansur ya yanke mata watanni shida a gidan yari ko tarar Naira dubu 50.

Ana gab da fara yaƙin neman zaɓen Barau.


Ana gab dab da fara yaƙin neman zaɓen Barau.

✍️ Abdul gaffar isah

Kwamitocin yaƙin neman zaɓen sanata Barau Jibrin, na kafafan sada zumunta na gab da fara aiki.

Hakan dai na ƙunshe cikin wata sanarwa da babban kwamitin ya fitar wadda Ibrahim Abdullahi Muhammad ya wallafa.

Sanarwar tace "wannan kwamiti na matasa da ɗalibai na shirin ƙirƙirar wasu kwamitocin dan nemawa Sen. Barau I. Jibrin ƙuriu a Dukkan ƙananan Hukumomin da yake wakilta.

Ibrahim yace "kwamitocin zasu yi aiki tuƙuru ba dare ba rana dan cimma burin su, ya kuma ƙara da cewa zasu fitar da Hazikan mutane waɗanda zasu iya nemowa jam'iyyar APC nasara a dukkan kujeru.

Zuwa yanzu dai akwai kwamitoci guda 3 na ɗalibai da ƴan midiya da zasu iya fara aiki.

1.  Bys Shuwaki  Daraktan Kafar sadarwa ta Zamani (Social Media)

2. Isyaku Abubakar Balan Daraktan Matasa

3. Yahaya Usman Kabo  Daraktan Dalibai

Ta'aziyya: Tambai ya miƙa saƙon ta'aziyyar sa ga iyalan Nura Bulak.

T


a'aziyya: Tambai ya miƙa saƙon ta'aziyyar sa ga iyalan Nura Bulak

✍️ Abdul gaffar isah

Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Hon. Ado Tambai Ƙwa ya miƙa saƙon ta'aziyyar sa ga iyalan Nura (Bulak)

Ya miƙa saƙon ta'aziyyar ne bisa wakilcin me magana da yawun sa Abdullahi Ishaq Bataye.

Nura Bulak ya rasu ne a daren jiya Alhamis an kuma yi jana'izar sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Bayan shafe watanni takwas, kungiyar ASUU ta janye yajin aikin da take yi.

  B


ayan sha fe watanni takwas, ƙungiyar ASUU ta janye yajin aiki

✍️ Abdul gaffar isah

Kungiyar malaman jami’a a Najeriya, ASUU ta sanar da jinkirta yajin aikin da mambobinta suka shafe wata takwas suna yi.

Dokta Chris Piwuna, mataimakin shugaban kungiyar ta ASUU ya tabbatar wa gidan rediyon BBC labarin, inda ya ce an janye yajin aikin ne da sanyin safiyar yau Juma’a, bayan da shugabannin ƙungiyar suka gana cikin dare a Abuja babban birnin kasar.

Kotun kolin Najeriya ta umarci kungiyar ta janye yajin aikin gabanin ta saurari daukaka karar da ta yi a gabanta.

Tun ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar malaman jami’o’in gwamnatin tarayyar Najeriya suka tsunduma cikin yajin aiki, suna neman gwamnatin ta biya musu wasu bukatu.

Thursday, October 13, 2022


Babu wani Gwamna daya tsira daga takobin Rarara.

✍️ Abdul gaffar isah

Babu wata tantama game da maganar Sheriff Almuhajir  wadda yayi ta tun kusan 2017.

Kano ta zama mafakar marasa mutunci, Yau abin mamaki akan idon Kanawa ya rufe, yayinda Rarara yazo ya zage duk shugabannin su.

Ya zagi Shekarau, duk da tarin halaccin da shekarau yayi masa.
Ya kira shekarau da Duna, Arnan ɓoye, Mallam me rawa da alkyabba, Ɓarawo, da sauransu.

Kwankwaso ya ɗan sha jinin jikin sa da shi, daga baya dai aka nuna masa cewa babu komai, ƙarshe yazo ya ciwa kwankwaso mutunci.
Ya kira shi da Tsula, da sauransu.

Yau kuma gashi yana zagin Ganduje, ya kuma kira shi da Hankaka da sauran cin mutumci.

lallai an gaida kanawa, ƙwararru a fagen siyasa.

Ni abinda ya shige min duhu shine:- Yanzu wanene me darajar da zamu kalla tunda duk shugabannin namu an zage su kuma mun yarda?