Saturday, October 15, 2022

Ƴan sanda sun kama shugaban APC da katin zaɓe sama da guda 300

Ƴan sanda sun kama shugaban APC da katin zaɓe sama da guda 300



✍️ Abdul gaffar isah

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano, ta sanar da cewa, jami’an yan sanda sun samu nasarar cafke wani mutum mai suna Aminu Ali Shana, wanda shugaban jam’iyyar APC ne a mazabar Yautan Arewa dake yankin karamar hukumar Gabasawa a jihar Kano, an kama shi da katin zabe sama da 300 na mutane da suke bi suna baiwa kudi suna karbewa.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren watsa labarai na NNPP Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, yace abinda shugaban APC ya aikata yaci karo da sashi na 21 da 22 sakin layi na 1, (a), (b) da kuma (c) cikin baka, na dokar zaɓe da aka yiwa kwaskwarima a shekarar 2022, saboda haka ne yasa shugaban NNPP na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, yayi umarnin daukar matakin shari’a akan wannan lamari.

Nasara fm Kano tace "Sanarwar ta ƙara da cewa, tuni aka tura lamarin zuwa sashen aikata manyan laifi (CID) domin fadada bincike, harma kuma jam’iyyar ta yaba da kokarin jami’an yan sanda, tare da kira a gare su, da su kara kaimi wajen bincike da cafke masu aikata laifi, musamman a yanzu da jam’iyyar APC ke kokarin dakile yawan masu zaɓe a jihar Kano, saboda ganin nasara na tare da NNPP.

No comments:

Post a Comment