Sunan fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, yayi ɓatan dabo a bangaren jarumai da masu nishadantarwa na kwamitin yakin neman zaɓen dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A baya bayan nan, an samu rashin jituwa tsakanin mawaki Rarara da bangaren gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ake zargin Rarara ya yiwa Ganduje habaici a cikin Waƙa, sakamakon zargin da yake kan cewa, anje domin cire sunansa cikin kwamiti, amma shi a wajensa, harkar Tinubu ba sai da takarda ba.

Rarara ya jaa layi da jam’iyyar APC a matakin jihar Kano, inda ya nuna goyon bayansa ga dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar ADP, wato dan majalisa Sha’aban Ibrahim Sharaɗa, abinda bai yiwa da yawa cikin magoya bayan jam'iyyar APC daɗi ba.