Friday, November 11, 2022

An gargadi Elun musk kan sauye-sauyen fasalin twitter.

 Wani babban kamfani da ke sa ido kan kafafen sada zumunta a Amurka, ya ce ya damu matuƙa kan halin da kamfanin sada zumunta na Tuwita ke ciki.

Babban jami'i a ofishin mai zaman kansa, ya ce sallamar ma'aikata da masu shirin barin aiki na sanya Tuwita cikin halin rashin tabbas da haɗarin take dokokin hukumar kasuwancin Amurka da hakan ka iya janyo cin kamfanin tarar makuɗan kuɗaɗe.

Hukumar ta gargadi shugaban Tuwita Elon Musk, da ya yi taka tsantsan, domin kuwa bai fi karfin doka ba.

Sai dai Mr Musk ya ce kamfanin ka iya durkushewa indai ba a bari ya ci gaba da sanya tallace-tallacen da wasu ke ganin ba su dace ba, kuma ma'aikatan da suka rage ba su da damar aiki daga gida.

-


BBC Hausa

Ya kamata a rage Albashin ƴan-majilisa dan biyan malaman jami'o'i. "Ndume

 S


anata Ali Ndume ya shawarci Gwamnatin tarayya ta zabtare Albashin ƴan majalisa da kashi 50 cikin 100 domin biyan malaman jami'o'i dake yajin aiki kuɗaɗen su.

Sanata Ndume dake wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattijai ya shaida haka ne a lokacin wani taro daya gudana a birnin Maidugurin.

Ya ƙara da cewa wannan abu ne daya shafi ƙasa baki ɗaya kuma dole a wasu lokutan a ɗau matakan ceto ƴan ƙasa da ilimi.

Kiran da Sanatan yayi na zuwa ne daidai lokacin da malaman jami'o'i ke ƙorafin cewa rabin Albashin su aka basu bayan sun janye yajin aikin.

Ɗan majalisar dai yace " lokaci yayi da Yakamata a shawo kan matsalolin dake durƙusar da fannin ilimi a Nigeriya.

A watan Oktoban daya gabata ne, ASUU ta janye yajin aikin data shafe wata takwas tana yi batare da biyan buƙatun ta daga wajen Gwamnatin tarayya ba.

Thursday, November 10, 2022

Naira tana farfaɗowa, bayan doguwar tazarar da aka bata.

 Darajar naira ta ƙaru da kashi 16.6% idan aka kwatanta da dalar Amurka a cikin kwana uku


.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ce an sayar da dalar Amurka ɗaya kan Naira 765 a kasuwar bayan fage a yammacin Alhamis.

Hakan na zuwa ne bayan da kasuwa ta buɗe ana sayar da nairar a kan 800 kan dala guda.

Masu hada-hadar kuɗi sun ce hakan ya faru ne sanadiyyar yadda aka rage neman dalar a kasuwa.

Haka nan kuma an fara samun wadatuwar dalar a kasuwar.

A makon da ya gabata dai, masu sana’ar canji a Najeriyar sun ce al’umma sun rinƙa turuwa zuwa wuraren canjin kuɗi bayan da babban bankin Najeriya ya bayar da sanarwar sauya wasu daga cikin takardun kuɗin ƙasar.

Darajar naira dai ta rinƙa faɗuwa a kasuwar bayan fage tun farkon 2022.

An dai rinƙa samun banbanci mai yawa tsakanin farashin dalar a hukumance da kuma na kasuwannin bayan fage.

Inda a hukumance farashin dalar ya kasance tsakanin naira 410 zuwa 450.

Wednesday, November 9, 2022

Twitter da facebook sun kori tarin ma'aikatan su.

 Twitter da facebook sun kori tarin ma'aikatan su.

A wannan makon Meta ya kori ma'aikatan sa na Facebook 11,000, Hakan na zuwa ne jim kaɗan bayan da Shima kanfanin Twitter ya sallami kusan dukan ma'aikatan sa a Gana ƙasa da sati biyu, bayan Biloniya Elun musk ya saye kanfanin.


Shekara ɗaya kenan da kamfanin ya buɗe ofishin nasa a Ganar wanda shine na farko a Afrika.

Korar ma'aikatan Ganar ya biyo bayan ɗunbin waɗanda kanfanin ya sallama a faɗin duniya, tun bayan saye shi da Elun musk yayi.

Baza a iya yimana kutse a Na'urorin mu ba a zaɓe me zuwa. - INEC

Ba za a iya kutse a na'urar tattara sakamakon zabe ba - INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta kara tabbatar wa 'yan kasar cewa ba za a iya yin kutse domin sauya bayanan da ke cikin na'urorin tattara sakamakon zabe ba.

Babban mataimakin shugaban hukumar mai lura da sashen fasahar zamani Lawrence Bayode ne ya tabbatar da haka a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani shiri na gidan Talbijin din Channels TV .

Yana mai cewa ba za a iya yi wa na'urar kutse a ranar zabe ba.

''Ina so in sake tabbatar da cewa mun yi duk abin da ya kamata domin tabbatar da cewa ba a yi wa na'urar kutse ba, za a kiyaye duka bayanan da ke cikin na'urar''.

“Bayan zaben, idan za a turo da bayanan zuwa babbar na'urarmu, za a kiyaye bayanan a lokacin da ake turo su, sannan bayan sun zo babbar na'urarmu,za a ci gaba da lura tare da kiyaye su'', in ji shi

Ya kara da cewa hukumar zaben ta tsaurara matakai domin tabbatar da cewa ba a yi kutse wa na'urorin ba.



Tuesday, November 8, 2022

Kotu ta aike da shugaban EFCC zuwa gidan yari

 Kotu ta aike da shugaban EFCC zuwa gidan yari


Mai shari’a Chizoba Oji na wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin aike shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC zuwa gidan yari bisa laifin ƙin bin umarnin kotu.



Alkalin ya kuma umurci Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasar da ya tabbatar da an aiwatar da hukuncin.


Oji ya ba da umarnin ne a ranar 28 ga Oktoba, in da a ka raba wa manema labarai a Abuja kwafin umarnin.


AVM Rufus Adeniyi Ojuawo ya gabatar da korafi a kan gwamnatin tarayya mai lamba FCT/HC/M/52/2021 a kara mai lamba FCT/HC/CR/184/2016.


AVM Ojuawo ta bakin lauyansa R.N. Ojabo, ya nemi umarnin daure Shugaban Hukumar EFCC a gidan yari.


Hakan ya bayu ne bisa rashin biyayyarsa ga kotu, ya kuma ci gaba da bijirewa umarnin kotun da ta bayar a ranar 21 ga Nuwamba, 2018.


Kotun ce ta umarci EFCC, Abuja da ta mayar wa wanda ya shigar da korafi motsa kirar Range Rover (Supercharge) SUV da kudin ta ya kai Naira miliyan N40.

Monday, November 7, 2022

Wani yaro ne yake tafiyar da Gwamnatin kasar nan ba Buhari ba. -- Aranfosu.

 

Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa Auwal lawan shuaibu Aranfosu yace "Ba shugaba Buhari ne yake tafiyar da harkokin ƙasar nan ba, wani yaro ne.


Hakan na ƙunshe ta cikin wani sharhi da ya wallafa a wani rubutu da Marzuk Ungogo ya wallafa a shafin sa na facebook.

Marzuk dai yayi magana ne kan tattaunawar da akayi da shugaba Buhari game da lamurran kasar nan, ya kuma nuna cewa Buhari be amsa tambayoyin da akayi masa dai-dai ba.

Jim kaɗan bayan wallafa rubutun ne Auwal Aranfosu ya rubuta nasa sharhin kamar haka: " Marzuq Ungogo Wani yaro ne fa yake tafiyar da Gwamnatin ba Baba Buhari ba sai dai muyi hakuri da abun da muka gani.

Rubutun nasa dai yaja cece kuce, se dai Aranfosu bai sake cewa komai ba.

Bazan biya kudi a hannu ba. -- Ganduje

 Ba na cikin gwamnonin da za su biya ma'aikata kuɗi hannu da dukiyar sata -- Ganduje


Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta musanta rahoton da ke cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cikin gwamnonin da ke ƙoƙarin halsta kuɗin haram ta hanyar biyan ma'aikata albashi a hannu maimakon ta banki.



Sashin Hausa na BBC ya rawaito cewa, Martanin na zuwa ne bayan wata kafar yaɗa labarai ta intanet ta yi iƙirarin cewa hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta saka wa Ganduje ido tare da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da Gwamnan Ribas Nyesom Wike saboda sun ɓoye garin biliyoyin kuɗi a wasu wurare.


Kafin haka, Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya faɗa wa Daily Trust cewa biyu daga cikin gwamnonin sun fito daga arewacin ƙasar, yayin da ɗaya ya fito daga kudanci, amma bai faɗi sunayensu ba.


"Duk da cewa EFCC ba ta faɗi sunan gwamnonin ba amma Sahara Reporters ta yi gaban kanta wajen yin iƙirari maras tushe," a cewar sanarwar da Kwamashinan Yaɗa Labarai na Kano Muhammad Garba ya fitar.


"Saboda haka ne ya nemi ta janye labarin tare da neman afuwa, wanda idan ba ta yi haka ba gwamnatin za ta kai ƙara kotu."


Sunday, November 6, 2022

Tabbas Ni ɗan gata ne kuma ɗan lele. - Abba Ganduje.

 Ɗan Takarar majalisar tarayya a mazaɓun D/tofa, Tofa, R/Gado Abba yace Tabbas ya yarda cewa shi ɗan gata ne kuma ɗan lele.


Abba Ganduje ya bayyana haka ne lokacin da yake miƙa sakon godiya ga waɗanda suka halarci taron Karrama shi da akayi a matsayin kwararren injiniya (FNSE).

Abba yace shidai be gayyaci kowa ba, saboda kada a maida gurin taron siyasa sai dai duk da haka mutanen DTR sunyi cicirindo a wannan wuri.

Abba Ganduje dai yace " bayan kammala wannan taron ɗaya daga cikin magoya baya ya bashi mota kyauta, sannan wani shima yayi masa alƙawarin ƙyautar wata motar, saboda haka Abba Ganduje yace lallai shi ɗan gata ne kuma ɗan lele.

Da yake jawabi game da takarar sa yace " Indai an zaɓe shi kuma yazo Gaisuwa sau ɗaya kawai to yafi wani ɗan Majilisar ko a'iya nan, kar akaiga ayyukan raya ƙasa su dama ajendar su kenan.

Sannan yace basu riƙa fita ralli ba batare da wata manufa ba, Tun a rallin su zasu rika kafa abinda zasu yi bayan sun samu Nasara.

Zasu bada gudunmawa sosai a ɓangaren ilimi da sauran su.

A ƙarshe ya ƙaddamar da kwamitocin da zasu taya shi yaƙin neman zaɓen 2023.

Saturday, November 5, 2022

Wani matashi ya kashe abokin sa anan Kano.

Wani matashi ya kashe abokin sa anan Kano.

Wani matashi mai shekara 15 ya cakawa abokinsa wuka bayan sunyi wata sa'insa, kan wasan suluka.


Lamarin ya faru ne a Karamar Hukumar Rimin Gado ta Jihar Kano a ranar Juma’a, inda matasan suka samu sabani a wajen wasan kwallon Sunuka.

A cewarsa, marigayin ne a lokacin takaddamar ya kalubalance shi da idan ya isa ya zo su je bayan gari domin a raba raini.

Shi kuma da ya tashi zuwa sai ya tafi da wukar da yake yankar rake.

“Muna zuwa sai ya shake ni, ya kama ni da duka, ni kuma da na ga haka, sai na fito da wukar na caka masa a kirji,” in ji shi.

An garzaya da Musbahu zuwa Asibitin Murtala na cikin birnin Kano, a inda suna zuwa, ko fita da shi daga mota ba a yi ba, da likita ya duba shi, ya ce ya mutu, in ji kawun marigayin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Madogara: Rahama Radio

Friday, November 4, 2022

EFCC ta ɗana tarko ga Gwamnonin da zasu biya albashi a hannu.

 A


na sa ido kan gwamnonin jihohi uku da ke kan karagar mulki a kan yunkurin da suka yi na karkatar da biliyoyin Naira ta hanyar biyan albashin ma’aikata. -  EFCC

Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce tana sa ido kan gwamnonin ƙasar uku sakamakon yunƙurinsu na halasta kuɗin haram da biliyoyin kuɗin da suka tara ta hanyar biyan ma'aikata albashi a hannu - maimakon ta banki.

Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya faɗa wa jaridar Daily Trust cewa dakarunsa za su ci gaba da kai samame kan 'yan canji game da zargin ɓoye dalar Amurka wanda hakan ke sa darajarta na hauhawa.

Duk da cewa Bawa bai faɗi sunan gwamnonin ba, ya ce biyu daga cikinsu daga arewacin Najeriya suke, inda ɗayan yake a kudanci.

Ya ce bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa gwamnonin sun kammala shirin fito da kuɗin ta hanyar biyan ma'aikatansu na jiha da garin kuɗi maimakon ta banki kamar yadda aka saba.

"Bari ku ji, a rahoton sirri da na samu jiya...tuni wasu gwamnonin jiha da suka ɓoye garin kuɗi a gidaje yanzu suka fara ƙoƙarin biyan albashi a hannu a jihohin nasu," in ji shi. .

Da aka tambaye shi ko EFCC za ta yi wa gwamnonin sammaci, Bawa ya ce suna dai saka musu ido zuwa yanzu.

EFCC na ɗaukar matakan ne a baya-bayan nan bayan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da shirin sake fasalin takardun naira na N200 da N500 da N1,000, inda ya ba da wa'adin kwana 47 ga 'yan ƙasar da su kai tsofaffin banki.

Wasu masana na ganin cewa hakan na da nasaba da ƙarin karyewar darajar nairar. CBN ya ce za a fara amfani da sabbin takardun kuɗin daga ranar 15 ga watan Disamban 2022.

Ilimi ya samu kaso mafi tsoka a cikin kudirin kasafin kudi na N245bn na Ganduje na karshe.


Ilimi ya samu kaso mafi tsoka a cikin kudirin kasafin kudi na N245bn na Ganduje na karshe.

✍️ Abdul gaffar isah

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya gabatar da kudurin kasafin kudi na shekarar 2023 na naira biliyan 245 wanda bangaren ilimi ya samu kaso mafi tsoka.


Gwamnan jihar Kano,  Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da kasafin kudi na Naira biliyan 245 na shekarar 2023 ga majalisar dokokin jihar domin amincewa.

Da ya ke gabatar da kasafin a yau Juma’a a Kano, Ganduje ya ce an sanya wa kasafin kuɗin, mai taken kasafi na ci-gaba da  wadata II, da nufin karfafawa tare da inganta rayuwar al’ummar jihar.

Ya ce kasafin ya kunshi manyan ayyuka  da za a kashe Naira biliyan 144, wanda ya nuna kashi 59 cikin 100 da kuma Naira biliyan 100 da za a kashe a harkokin yau da kullum, wanda ya nuna kashi 41 cikin 100.

Gwamnan ya ce bangaren ilimi shi ne ya fi ɗaukar kaso mafi tsoka, inda a ka ware masa Naira biliyan 62, wanda ya nuna kashi 27 cikin 100 fiye da adadin da UNESCO da Majalisar Dinkin Duniya suka ba da shawarar a rika fitar wa, inda ya ce za a fitar da kudaden ne wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsare da nufin tabbatar da ingantaccen ilimi a dukkan matakai.

Ya ce za a kuma yi amfani da wani bangare na kudaden wajen inganta shirin ilimi kyauta kuma dole a jihar.

Ganduje ya ce an ware wa fannin lafiya Naira biliyan 39.1, albarkatun ruwa Naira biliyan 15, ɓangaren sufuri Naira biliyan 8.6, fannin noma Naira biliyan 19.9 da ayyuka da kayayyakin more rayuwa Naira biliyan 35.

Ya bukaci ‘yan majalisar su tabbatar da  gaggauta amincewa da kasafin kudin domin baiwa gwamnati damar ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar.

Gwamnan ya kuma bukaci matasa da su guji duk wani tashin hankali musamman ganin zaben 2023 ya kara kusanto.

A nasa jawabin shugaban majalisar, Alhaji Hamisu Chidari, ya baiwa gwamnan tabbacin yin gaggawar zartar da kasafin kudin domin samun damar darewa kan kasafin kudin watan Janairu zuwa Disamba.

Chidari ya bukaci Ma'aikatun Gwamnati da Hukumomi (MDAs) da su kasance a shirye don kare kasafin kudi a majalisar.

Kakakin majalisar ya kuma yaba wa gwamnan bisa kokarin da ya ke yi a bangaren samar da ababen more rayuwa, tsaro, lafiya da ilimi.


Abba Ganduje ya Siyawa mutanen kaburma maƙabarta.

 E


ngr Abba Ya Siyawa  Al'ummar Garin Kaburma Makabarta Ta Zun Zurutun Kuɗi Naira Duba Ɗari Takwas 800,000 dake Mazaɓar Tumfafi Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Abba Ganduje Ya Saya Musu Filin Ne saboda Maƙabartar Dake Wanna gari Ta Cika.

Tun da Fari dai mutanen Wannan Gari Sune suka Mika Kokensu Na Bukatar Saya Musu Wannan Makabarta Nan Take Ɗan Takarar Ya Tura Wakilai Domin Duba Inda In Suke Bukatar A Saya Musu Sannan Kuma Ya Bada Wannan Kuɗi Domin A Biya Wannan Makabarta.

Al'ummar Gari Sunyi Masa Godiya Da Fatan Alhairi Da Fatan Dacewa Da Abunda Aka Saka Gaba.

Engr Ya Samu Wakilcin Ado Abdu Yunfuwa Da Alh Yahaya Usman Tumfafi CPC Chiarman Dawakin Isa Musa Namaradu Comr Rabiu Abubakar Tumfafi Da Sauran Al'Umma Baki Ɗaya.

Bam’ Ya Kashe Mutum 2 A Kaduna.

 Bam’ Ya Kashe Mutum 2 A Kaduna

Wasu mutum biyu sun mutu yayin da wani abu da aka binne ya fashe ya kuma tashi da su a Karamar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna.


Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na rana a jiya Alhamis.

Motar wadanda abin ya rutsa da su ta bi ta kan abin fashewar da ake zargin ’yan ta’adda ne suka dasa a Zangon Tofa a yankin Kabrasha.

An rawaito cewa mutanen kauyen na jigilar amfanin gonar da suka girbe lokacin da lamarin ya afku.

Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ayyana mutum biyu a matsayin wadanda suka rasa rayukansu; Babajo Alhaji Tanimu da Safiyanu Ibrahim.

A cewarsa, Gwamnatin Jihar na bincike kan lamarin.

Ya kuma ce Gwamnan Jihar, Nasiru El-Rufai, ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa.

An Rabawa mata Dabbobin kiwo a Jigawa.

 Bankin duniya tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa , sun raba dabbobi 381 ga mata 127 dake kananan hukumomin Gumel da Maigatari da Gagarawa da kuma Sule tankarkar domin yin kiwo a gidajensu.


Darakta a ma'aikatar mata ta Jihar Jigawa Hajia Adama Umar Zandam ce ta bayyana hakan a madadin babbar sakatariyar ma’aikatar a garin Gumel.

Hajiya Adama tace an zabo mata masu karamin karfi daga kundin rijistar da ma'aikatar take dashi domin samun awakin,
Inda ta kara da cewar mata 30 ne suka sami awaki 90 a karamar hukumar Gagarawa, sai mata 20 da suka sami awaki 60 a karamar hukumar sule tankarkar sai mata 22 da suka samu awaki 66 a kananan hukumomin Gumel da Maigatari.
Wakilin Nasara Radio a jahar jigawa Muhammad Sa'idu Limawa ya rawaito cewar Hajiya Adama Tace "An raba awakin ne domin ragewa matan radadin dokar kulle da aka sanya a lokacin bullar cutar corona da nufin bunkasa tattalin arzikinsu.

Thursday, November 3, 2022

Waiwaye: Babu mai gaskiya kamar Annabi Muhammadu S.A.W - Javier Hernandez

 Ni ba Musulmi ba ne, Amma Na san Annabi Muhammadu Shi ne Mutumin da Yafi Kowa a Duniya Inji Chicharito


Daga: Abdul gaffar isah

Duk waɗanda suka san shi saidai su faɗi alheri, nagarta da kuma kyawawan halayyarshi.

Waɗanda suka karanta tarihinshi a natse, suna yawan yabawa tare da jinjinawa irin rayuwar da ya yi a duniya.

Chicharito ɗan wasan kwallon ƙafa ne na ƙasar Mexico wanda ya bayyana Annabi (SAW) a matsayin mutum mafi nagarta a duniya, duk da kuwa kirista ne.

Waɗanda suka sanshi ko suka karanta wani abu a kan shi, sun san irin albarkatacciyar rayuwar da yayi.

An gano cewa ƴan kwallo da sanannu a duniya na nuna mishi soyayya saboda tarihin shi da suka samu. Wanna ba kowa bane sai Annabi Muhammad SAW.

An turo shi ne zuwa ga mutane baki daya. Ba Annabin musulmai ba ne kaɗai, dukkan mutane ne za a musu hisabi da zuwanshi.

Wani babban dan wasan kwallon kafa daga kasar Mexico, Javier Hernandez Balcazar wanda aka fi sani da ‘Chicharito’ ya shiga sahun masoya Annabi.

A daya daga cikin wallafar da yayi a shafinshi na tuwita, ya bayyana irin kaunar da ya ke wa Manzon ta yadda ya ce shi ne mutum mafi nagarta a duk duniya.

Duk da ko Chicharito mabiyin Katolika ne, rayuwar Annabi ta matuƙar burgeshi har ya bayyana abinda ke ranshi.

Chicahrito ne ɗan kwallon kafa na farko a ƙasar Mexico da ya yi wasa da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United. Ya halarci wasan gasar kwallon kafa ta duniya a 2010. An karamashi bayan da yaci kwallaye 7.

Abun farin ciki ne da jin daɗi idan kaga wadannan mutanen suna karanta tarihin Annabi kuma sun bayyana kaunarsu gareshi. Allah ya kara tabbatar da mu cikin addinin musulunci da shiriya ta gaskiya.

Wednesday, November 2, 2022

An bawa Abba Ganduje lambar yabo.

 A


n Karrama Engr Umar Ganduje a Matsayin Kwararran Injiniya Tare da Lambar Girmamawa ta FNSE.

Mai Girma Dan Takarar Majalisssar Tarayya Engr Umar Abdullahi Umar Ganduje , ya  Samu Lambar Girmamawa a Matsayin Cikakken Engineer Wato FNSE Wanda Kungiyar Injiniyoyi ta Kasa Wato (Nigerian Society of Engineers) ta Tabbatar Dashi Tare da Mika masa Lambar Girmamawa, A wani Biki da Suka Gudanar a Karo na 21a Dakin Taro na Hotel din Chida Dake Utako a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Engr Ganduje, An Haife shi a Karamar Hukumar Dawakin Tofa Dake Jihar Kano, ya Kammala Karatun Digirinsa na Farko a Fannin Wutar Lantarki a Jami'ar Sharja Dake Daular Larabawa, Daga Bisa ya kara Samun Digiri na Biyu (Master's) Tare da Sakamako Mafi Daraja na Daya Wato Distinction a Fannin Sadarwa a Jami'ar Buckinghamshire Dake Kasar England,  Baya ga Samun Shedar Kammala Karatun Diploma a Fannin Sadarwa da wayoyin Hannu a Makarantar Commonwealth a Shekarar 2018.

Engr Ganduje, ya Shugabanci Gurabe Dabam Dabam Wanda Suka Danaganci Injiniyoyi Tare da Shiga Kungiyoyin Sadarwa, Engr Ganduje, ya Zama Babban Mataimaki Wato Senior Legislative Aide, a Offishin Mataimakin Shugaban Majalisssar Tarayya ta Kasa Wato Deputy Speaker Office.

Kafin Wannan, Engr Ganduje, Yayi aiki a Maaikatar Sadarwa ta NCC Tare da Rike Manager a Sashen USPF a Maaikatar Baki Daya, baya ga Haka Ya Samu kwarewar Aiki ta Shekaru Goma Tare da Harkar Gwagwarmaya a Fannoni Dabam Dabam.

Yanzu Haka Engr Ganduje, Shine Dan Takarar Majalisssar Tarayya Wanda zai Wakilci Kananan Hukumomin Dawakin Tofa Rimingado da Tofa Daga Jihar Kano a Jamiyar Apc da Yaddar Allah.

Taron ya Samu Halattar Mai Dakin Gwamnan Kano Prof Hafsat Abdullahi Ganduje,  Direktocinsa Karkashin Direkta General Dr Junaidu Yakubu Muhd, Kwamishinoni, Dan Takarar Majalisssar Jiha Hon Salisu Musa Gulu, Shugabannin Kananan Hukumomin Dawakin Tofa da Tofa, Masu Bawa Gwamna Shawara a Fannoni Dabam Dabam. Yau
TALATA 1 November 2022.

Tuesday, November 1, 2022

DAMSA tayi SANITATION

 DAMSA tayi SANITATION



✍️ Abdul gaffar isah


Kungiyar DAWAKIN TOFA MEDICAL STUDENTS ASSOCIATION (DAMSA) ta gudanar da Tsaftar muhalli a Dawakin Tofa.

DAMSA dai kungiya ce ta Ɗaliban lafiya dake ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, suna ayyuka bada agaji ga al'umma da kuma temakawa marasa ƙarfi musamman a ɓangaren lafiya.

A ranar Lahadin data gabata ƙungiyar ta gudanar da Tsaftar muhalli wanda aka fi sani da (SANITATION).

Wannan dai shine karo na farko da ƙungiyar ta gudanar da wannan aiki, se dai tasha alwashin cigaba da wannan aiki lokaci zuwa lokaci.

Shugaban ƙungiyar Muhammad lawan Musa yace "sunyi wannan aiki ne biyo bayan rashin tsaftace magudanan ruwa, da tituna, da kasuwanni, da wuraren cin abinci da sauransu.

A ƙarshe dai Kungiyar tayiwa gangamin aikin take da
(RANAR TSAFTAR MUHALLI (SANITATION) TA DAWAKIN TOFA)

Dokokin Babban Bankin ƙasa CBN na ƙara saka mutanen arewa a talauci. Sherif Almuhajir.

Dokokin Babban Bankin ƙasa CBN na ƙara saka mutanen arewa a talauci. Sherif Almuhajir.

✍️ Abdul gaffar isah

Shugaban Bankin manoma na jihar Yobe Dr. Sherrif Almuhajir yace Dokokin Babban bankin kasa CBN suna ƙara saka mutanen arewa a cikin tsanani, a lokacin da suke ƙara azurta mutanen kudu.

Almuhajir ya bayyana haka ne ta cikin wani Faifan Bidiyo da ya wallafa a shafin sa na facebook a daren jiya Litinin.

Yace "wasu watanni shida da suka gabata  yayi bayani kan Wasu dokokin CBN da Development Bank of Nigeria da sauran Bankuna yadda yake ganin tsare-tsaren su  suna da tsauri ga ƴan Arewa musamman ma musulmin su, yace "hakan na ƙara tsananta talauci a arewa yayinda yake ƙara azurta mutanen kudu.

Almuhajir yace "Dokokin dai daga nan zuwa shekar 100 babu yadda za'ayi ɗan arewa yaji daɗin tsarin tattalin arzikin Nigeriya muddin idan ba'a duba su ba.

Dr. Sherif dai yace "Tabbas akwai son rai a tsare-tsaren bankin se dai yana kira ga masu Ruwa da tsaki su ƙara duba tsare-tsaren da kyau.

Dayake jawabi Game da canjin kuɗin da ake shirin yi nan ba da daɗewa ba, Dr. Sheriff Almuhajir yayi kira ga CBN daya ƙara lokaci, saboda mutanen arewa dayawa basu saba da mu'amala da banki ba, kuma idan akayi shi kamar yadda aka tsara ze daɗa karya wasu ƴan kasuwar arewacin kasar, ya ƙara da cewa "zaka iya samun wanda yake da miliyan 500 amma kuɗi hannu, yanzu wannan idan kace yaje ya saka su a banki lokaci ɗaya tabbatas hukumar NFIU seta bincike shi, alhali kuma halattattun kudade ne.

Sannan ya bayyana cewar akwai waɗanda su kuma sunyi nisa da Bankin ne shiyasa basama ajiye kuɗin su abanki, ya ƙara da cewa  "A jihar Yobe kananan hukumomi 4 ne suke da bankuna tayaya zakace kowa ya maida kuɗi banki bayan har yanzu wasu basu sanshi ba.

Daga cikin abubuwan da masanin ya bayyana waɗanda ke ƙara karya tattalin arzikin Arewa " Development Bank of Nigeria banki ne da akayi shi dan ƴan Nigeriya, yace "A shekarar data gabata sun raba kuɗi ₦ biliyan 400 da 82 a Nigeriya, amma kaso Hamsin da bakwai an kaisu south/west na kudancin Nageriya ɓangaren yarabawa, yayin aka kai kaso goma sha takwas south/south se kuma kaso tara an kaishi south/East.

Dr. Sherrif yace daya haɗa lissafin kudin se yaga an kai biliyan 400 gaba ɗaya kudancin kasar, kuma yace suma ƴan Arewa suna zuwa nema domin shi kansa yace yaje dan karɓowa Jihar Yobe, amma an saka musu dokoki masu tsauri waɗanda ba zasu ciku ba, se dai ya bawa mutani yobe haƙurin cewa baza su samu ba.

Amma gaba ɗaya North/East na arewacin Najeriya kaso ɗaya kawai suka samu a cikin 100, wanda adadin nasa yakai ₦ biliyan 4 da 820, yayinda sukuma North/west a Arewacin kasar suka samu kaso biyar wanda adadin yakai ₦ biliyan 24 da miliyan 100.

Yace Tabbas akwai kuskure da son rai cikin wannan tsari gaba ɗaya arewa basu wuce kaso bakwai ba yayinda Lagos ita kaɗai ta samu ₦ biliyan 247.

Yace dole a canja Dokokin tsarin bankin ta yadda zasu yi daidai da addinin mu, mu'amalar mu, tsarin mu, dakuma yadda zamu iya. bankunan nan da ake assasawa  kudaɗen ƴan Najeriya ne aciki, se dai yayi wani zargin cewa idan an zuba kuɗaɗen ana zagayewa aturawa ƴan kudu suyi kasuwanci dasu.