Friday, November 11, 2022

An gargadi Elun musk kan sauye-sauyen fasalin twitter.

 Wani babban kamfani da ke sa ido kan kafafen sada zumunta a Amurka, ya ce ya damu matuƙa kan halin da kamfanin sada zumunta na Tuwita ke ciki.

Babban jami'i a ofishin mai zaman kansa, ya ce sallamar ma'aikata da masu shirin barin aiki na sanya Tuwita cikin halin rashin tabbas da haɗarin take dokokin hukumar kasuwancin Amurka da hakan ka iya janyo cin kamfanin tarar makuɗan kuɗaɗe.

Hukumar ta gargadi shugaban Tuwita Elon Musk, da ya yi taka tsantsan, domin kuwa bai fi karfin doka ba.

Sai dai Mr Musk ya ce kamfanin ka iya durkushewa indai ba a bari ya ci gaba da sanya tallace-tallacen da wasu ke ganin ba su dace ba, kuma ma'aikatan da suka rage ba su da damar aiki daga gida.

-


BBC Hausa

Ya kamata a rage Albashin ƴan-majilisa dan biyan malaman jami'o'i. "Ndume

 S


anata Ali Ndume ya shawarci Gwamnatin tarayya ta zabtare Albashin ƴan majalisa da kashi 50 cikin 100 domin biyan malaman jami'o'i dake yajin aiki kuɗaɗen su.

Sanata Ndume dake wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattijai ya shaida haka ne a lokacin wani taro daya gudana a birnin Maidugurin.

Ya ƙara da cewa wannan abu ne daya shafi ƙasa baki ɗaya kuma dole a wasu lokutan a ɗau matakan ceto ƴan ƙasa da ilimi.

Kiran da Sanatan yayi na zuwa ne daidai lokacin da malaman jami'o'i ke ƙorafin cewa rabin Albashin su aka basu bayan sun janye yajin aikin.

Ɗan majalisar dai yace " lokaci yayi da Yakamata a shawo kan matsalolin dake durƙusar da fannin ilimi a Nigeriya.

A watan Oktoban daya gabata ne, ASUU ta janye yajin aikin data shafe wata takwas tana yi batare da biyan buƙatun ta daga wajen Gwamnatin tarayya ba.

Thursday, November 10, 2022

Naira tana farfaɗowa, bayan doguwar tazarar da aka bata.

 Darajar naira ta ƙaru da kashi 16.6% idan aka kwatanta da dalar Amurka a cikin kwana uku


.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ce an sayar da dalar Amurka ɗaya kan Naira 765 a kasuwar bayan fage a yammacin Alhamis.

Hakan na zuwa ne bayan da kasuwa ta buɗe ana sayar da nairar a kan 800 kan dala guda.

Masu hada-hadar kuɗi sun ce hakan ya faru ne sanadiyyar yadda aka rage neman dalar a kasuwa.

Haka nan kuma an fara samun wadatuwar dalar a kasuwar.

A makon da ya gabata dai, masu sana’ar canji a Najeriyar sun ce al’umma sun rinƙa turuwa zuwa wuraren canjin kuɗi bayan da babban bankin Najeriya ya bayar da sanarwar sauya wasu daga cikin takardun kuɗin ƙasar.

Darajar naira dai ta rinƙa faɗuwa a kasuwar bayan fage tun farkon 2022.

An dai rinƙa samun banbanci mai yawa tsakanin farashin dalar a hukumance da kuma na kasuwannin bayan fage.

Inda a hukumance farashin dalar ya kasance tsakanin naira 410 zuwa 450.

Wednesday, November 9, 2022

Twitter da facebook sun kori tarin ma'aikatan su.

 Twitter da facebook sun kori tarin ma'aikatan su.

A wannan makon Meta ya kori ma'aikatan sa na Facebook 11,000, Hakan na zuwa ne jim kaɗan bayan da Shima kanfanin Twitter ya sallami kusan dukan ma'aikatan sa a Gana ƙasa da sati biyu, bayan Biloniya Elun musk ya saye kanfanin.


Shekara ɗaya kenan da kamfanin ya buɗe ofishin nasa a Ganar wanda shine na farko a Afrika.

Korar ma'aikatan Ganar ya biyo bayan ɗunbin waɗanda kanfanin ya sallama a faɗin duniya, tun bayan saye shi da Elun musk yayi.

Baza a iya yimana kutse a Na'urorin mu ba a zaɓe me zuwa. - INEC

Ba za a iya kutse a na'urar tattara sakamakon zabe ba - INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta kara tabbatar wa 'yan kasar cewa ba za a iya yin kutse domin sauya bayanan da ke cikin na'urorin tattara sakamakon zabe ba.

Babban mataimakin shugaban hukumar mai lura da sashen fasahar zamani Lawrence Bayode ne ya tabbatar da haka a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani shiri na gidan Talbijin din Channels TV .

Yana mai cewa ba za a iya yi wa na'urar kutse a ranar zabe ba.

''Ina so in sake tabbatar da cewa mun yi duk abin da ya kamata domin tabbatar da cewa ba a yi wa na'urar kutse ba, za a kiyaye duka bayanan da ke cikin na'urar''.

“Bayan zaben, idan za a turo da bayanan zuwa babbar na'urarmu, za a kiyaye bayanan a lokacin da ake turo su, sannan bayan sun zo babbar na'urarmu,za a ci gaba da lura tare da kiyaye su'', in ji shi

Ya kara da cewa hukumar zaben ta tsaurara matakai domin tabbatar da cewa ba a yi kutse wa na'urorin ba.



Tuesday, November 8, 2022

Kotu ta aike da shugaban EFCC zuwa gidan yari

 Kotu ta aike da shugaban EFCC zuwa gidan yari


Mai shari’a Chizoba Oji na wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin aike shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC zuwa gidan yari bisa laifin ƙin bin umarnin kotu.



Alkalin ya kuma umurci Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasar da ya tabbatar da an aiwatar da hukuncin.


Oji ya ba da umarnin ne a ranar 28 ga Oktoba, in da a ka raba wa manema labarai a Abuja kwafin umarnin.


AVM Rufus Adeniyi Ojuawo ya gabatar da korafi a kan gwamnatin tarayya mai lamba FCT/HC/M/52/2021 a kara mai lamba FCT/HC/CR/184/2016.


AVM Ojuawo ta bakin lauyansa R.N. Ojabo, ya nemi umarnin daure Shugaban Hukumar EFCC a gidan yari.


Hakan ya bayu ne bisa rashin biyayyarsa ga kotu, ya kuma ci gaba da bijirewa umarnin kotun da ta bayar a ranar 21 ga Nuwamba, 2018.


Kotun ce ta umarci EFCC, Abuja da ta mayar wa wanda ya shigar da korafi motsa kirar Range Rover (Supercharge) SUV da kudin ta ya kai Naira miliyan N40.

Monday, November 7, 2022

Wani yaro ne yake tafiyar da Gwamnatin kasar nan ba Buhari ba. -- Aranfosu.

 

Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa Auwal lawan shuaibu Aranfosu yace "Ba shugaba Buhari ne yake tafiyar da harkokin ƙasar nan ba, wani yaro ne.


Hakan na ƙunshe ta cikin wani sharhi da ya wallafa a wani rubutu da Marzuk Ungogo ya wallafa a shafin sa na facebook.

Marzuk dai yayi magana ne kan tattaunawar da akayi da shugaba Buhari game da lamurran kasar nan, ya kuma nuna cewa Buhari be amsa tambayoyin da akayi masa dai-dai ba.

Jim kaɗan bayan wallafa rubutun ne Auwal Aranfosu ya rubuta nasa sharhin kamar haka: " Marzuq Ungogo Wani yaro ne fa yake tafiyar da Gwamnatin ba Baba Buhari ba sai dai muyi hakuri da abun da muka gani.

Rubutun nasa dai yaja cece kuce, se dai Aranfosu bai sake cewa komai ba.