Wednesday, October 19, 2022

Dubu biyar zan riƙa biyan ƴa-ƴa na a wata.

 Dubu biyar zan riƙa biyan ƴa-ƴa na a wata.

✍️ Abdul gaffar isah

Wata mata ta kai tsohon mijinta ƙara, gaban Alkali bisa zargin gaza ciyar da ƴaƴan sa.


Matar dai ta kai tsohon mijin nata ne gaban me Shari'a inda take zargin sa da gaza ciyar da ƴaƴan sa, bayan da yake suka rabu.

Tace dubu 7500 yake bawa yaran su uku duk wata.

Me Shari'a ya tambayi magidancin gaskiyar lamarin, Nan take kuma ya amsa abinda ake zargin sa dashi, se dai yace iya ƙarfin sa kenan.

Me Shari'a Muhammad Sharif yacewa magidancin yayi ƙari kan abinda yake bayarwa, se dai ankai ruwa rana dashi kafin daga bisani ya ƙara ɗari biyar, wato yara biyu dubu biyar, se kuma babban su dubu uku.

Me Shari'a yace ya ɗaga ƙarar zuwa sati me zuwa, se dai yacewa wannan magidancin yazo da shirin sa.

No comments:

Post a Comment