Monday, October 31, 2022

Tambai ya yabawa Ganduje kan ayyukan raya ƙasa.

 Tambai ya yabawa Ganduje kan ayyukan raya ƙasa.

✍️ Abdul gaffar isah

Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Hon. Alh Ado Tambai Ƙwa ya yabawa Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje bisa ayyukan raya ƙasa da yayi a Dawakin Tofa.


Shugaban yayi godiyar ne lokacin da yake jawabin sa a gaban me girma Gwamnan jihar Kano da kuma mai martaba sarkin Bichi Alh DR. Nasiru Ado Bayero a yayin ƙaddamar da buɗe asibitin ido a Dawakin Tofa.

Tambai yace Babu shakka dole a yabawa Ganduje kan ayyukan jigaban al'umma a Dawakin Tofa.

Ya fara da lissafa ayyukan tituna, da gyara wasu daga cikin makarantun Gwamnati, da kai makarantar sojin ruwa, duka a Dawakin Tofa.

Sai dai yayi wani roƙo ga Gwamnan kan tabbatar da Makarantar kiwon lafiya wadda yace ya bayyana tafiyar tata da tafiyar hawainiya.

Yace "suna ƙoƙarin kai Ɗalibai makarantu da dama a wasu garuruwa, wanda idan akwai makarantar a Dawakin Tofa zasu sami sauƙi.

No comments:

Post a Comment