Friday, November 4, 2022

An Rabawa mata Dabbobin kiwo a Jigawa.

 Bankin duniya tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa , sun raba dabbobi 381 ga mata 127 dake kananan hukumomin Gumel da Maigatari da Gagarawa da kuma Sule tankarkar domin yin kiwo a gidajensu.


Darakta a ma'aikatar mata ta Jihar Jigawa Hajia Adama Umar Zandam ce ta bayyana hakan a madadin babbar sakatariyar ma’aikatar a garin Gumel.

Hajiya Adama tace an zabo mata masu karamin karfi daga kundin rijistar da ma'aikatar take dashi domin samun awakin,
Inda ta kara da cewar mata 30 ne suka sami awaki 90 a karamar hukumar Gagarawa, sai mata 20 da suka sami awaki 60 a karamar hukumar sule tankarkar sai mata 22 da suka samu awaki 66 a kananan hukumomin Gumel da Maigatari.
Wakilin Nasara Radio a jahar jigawa Muhammad Sa'idu Limawa ya rawaito cewar Hajiya Adama Tace "An raba awakin ne domin ragewa matan radadin dokar kulle da aka sanya a lokacin bullar cutar corona da nufin bunkasa tattalin arzikinsu.

No comments:

Post a Comment