Saturday, November 5, 2022

Wani matashi ya kashe abokin sa anan Kano.

Wani matashi ya kashe abokin sa anan Kano.

Wani matashi mai shekara 15 ya cakawa abokinsa wuka bayan sunyi wata sa'insa, kan wasan suluka.


Lamarin ya faru ne a Karamar Hukumar Rimin Gado ta Jihar Kano a ranar Juma’a, inda matasan suka samu sabani a wajen wasan kwallon Sunuka.

A cewarsa, marigayin ne a lokacin takaddamar ya kalubalance shi da idan ya isa ya zo su je bayan gari domin a raba raini.

Shi kuma da ya tashi zuwa sai ya tafi da wukar da yake yankar rake.

“Muna zuwa sai ya shake ni, ya kama ni da duka, ni kuma da na ga haka, sai na fito da wukar na caka masa a kirji,” in ji shi.

An garzaya da Musbahu zuwa Asibitin Murtala na cikin birnin Kano, a inda suna zuwa, ko fita da shi daga mota ba a yi ba, da likita ya duba shi, ya ce ya mutu, in ji kawun marigayin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Madogara: Rahama Radio

No comments:

Post a Comment