Thursday, October 20, 2022

Amurka zata temakawa Nigeriya.

 Ƙasar Amurka za ta taimaka wa mutanen da ambaliya ta shafa a Najeriya


Daga: Abdul gaffar isah

Gwamnatin Amurka za ta bayar da taimakon da ya kai na dala miliyan 1 ga mutanen da ambaliya ta yi wa barna a Najeriya.

Tallafin da za ta bayar ta hanyar hukumarta ta raya kasashe masu tasowa (USAID), zai kasance na gaggawa.

Ruwan sama mai tsanani da ya haddasa ambaliya ya janyo illa ga kusan mutum miliyan 2.8 a fadin kasar.

Gidaje da dama sun lalace ko ma sun rushe a sanadiyyar matsalar wadda ta tashi miliyoyin mutane daga gidajensu.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurkar ya fitar a Abuja a yau Alhamis.

Amurkar ta kuma ce ta damu da yuwuwar ruwan ambaliyar da ya taru a wurare zai iya kara hadarin kamuwa da cutar amai da gudawa da sauran cutuka da ake dauka a ruwa, a jihohin Adamawa da Borno da Yobe.

A wadannan jihohin an samu barkewar cutar kwalara a watan Agusta da Satumba, kuma ta kama mutum akalla 7,750 in ji sanarwar.

A wannan shekarar da ake ciki an samu rahotannin bullar cutar ta amai da gudawa a jihohi 31 daga cikin 36 na Najeriyar.

Kadaura ta rawaito cewa  jakadiyar Amurkar a Najeriya Mary Beth Leonard, ta ce suna cike da jimami kan wadanda ambaliyar ta shafa da suka rasa abubuwa da dama – hanyoyin rayuwarsu da gidajensu har ma da ‘yan uwansu.

Ta kara da cewa Amurka za ta ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Najeriya a wannan mawuyacin lokaci.

Sannan za ta yi aiki tare da hukumomin kasar yayin da ake sa ran samun karin ruwan sama da ambaliya a watan Nuwamba, a wasu sassan kasar saboda sauyin yanayi da rashin magudanun ruwa, da nufin samar da karin taimako idan akwai bukatar haka.

No comments:

Post a Comment