Friday, October 21, 2022

Sama da mata 800,000 a Nigeriya ke fama da matsalar yoyon fitsari. - UNFPA

 UNFPA: Sama da Matan Najeriya 800,000 ke fama da yoyon fitsari

✍️ Abdul gaffar isah

Asusun kula da yawan al'umma na Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA) ya ce sama da mata 800,000 ne ke fama da cutar yoyon fitsari, yawancinsu a yankin arewacin kasar.


Dr. Danladi Idrissa ne ya bayyana hakan a yayin bikin yaye wasu mutane 50 da suka kamu da cutar yoyon fitsari a cibiyar raya mata da ke Adamawa a ranar Alhamis.

Dokta Idrissa ya bayyana cewa UNFPA tare da hadin gwiwar gidauniyar Fistula da ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma sun gudanar da aikin tiyatar kusan mutane 265 daga cikinsu 225 sun warke.

Ya ce sauran 40 din na bukatar a yi babban aikin tiyata wanda ba za a iya gudanar da shi a jihar ba saboda rashin kayan aiki masu inganci.

Ya kuma bukaci iyaye da kada su aurar da ‘yan mata domin kare su daga kamuwa da yoyon fitsari a lokacin haihuwa da kuma hana su kashe kansu.

“Mata na fama da yoyon fitsari idan mafitsara ta fashe a lokacin haihuwa.  Ya zama ruwan dare a yankin arewacin kasar nan saboda aurar da yara kanana, rashin kula da haihuwa, da haihuwa a gida su ne manyan abubuwan da ke haifar da yoyon fitsari”.

“Wadannan matan sun fuskanci mummunan rauni na tunani, saboda yawancin an yi watsi da su kuma rayuwa ta zamar musu kalubale.  Idan suka faraá wari, suna samun matsala a cikin aurensu.

Musa Isa, wanda ya kafa gidauniyar Fistula a Najeriya, ya ce an baiwa wadanda suka tsira daga yoyon fitsari horo na tsawon watanni 4 na horon kasuwanci ya kara da cewa an basu kayan aikin ne don karfafawa gyiwa don dogaro da kai.

Kwamishinan harkokin mata da ci gaban al’umma, Hon.  Lami Patrick ta yaba da kokarin gidauniyar yoyon fitsari da UNFPA kan wannan daukin tare da alkawarin samar da hanyar da za ta taimaka wa sauran majinyata.

No comments:

Post a Comment