Saturday, October 29, 2022

An jibge tarin Net ɗin sauro a Dawakin-Tofa.

 An jibge tarin Net ɗin sauro a Dawakin-Tofa.

✍️ Abdul gaffar isah

Ma'aikatar kiwon lafiya ta ƙasa haɗin gwiwa da kungiyar CRS na Shirin raba gidan sauro, a wani yunƙurin su na Shirin yaƙi da cutar maleriya.



Cutar maleriya dai itace cuta mafi halaka mafi yawan cin mutanen Afrika awani binciken kwakwaf da akayi shekaru da dama, a shekarar 2019 annobar korona ta bulla a duniya amma duk da haka batayi illa ga mutanen Afrika kamar zazzabin cizon sauro ba.

Wannan ne yasa Hukumar daka kula da sha'anin lafiya ta ƙasa da ta jiha haɗin gwiwa da kungiyoyin agaji suke raba gidan sauro dan rage yawan masu kamuwa da maleriyar.

Yau kwana 4 kenan da aka fara kawo gidan sauron wajen ajiya dake Ofisoshin Hisba a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, an kuma kawo Babbar Mota (Trela) 2, washe gari ma aka kawo 2 se jiya shima an kawo 2 wanda jimillar su ya haɗa mota shida kenan.

Me kula da aikin kawo Net ɗin ya sheda min cewa "Wani bincike ya tabbatar da mafi yawan mata da yara da mata sunfi kamuwa da cutar kuma sunfi saurin mutuwa.

Se dai be sheda min sanda za'a fara raba Net ɗin ba, saboda yace "Gaba ɗaya ƙasa ne baki ɗaya.

No comments:

Post a Comment