Saturday, October 29, 2022

Muna kira da Gwamnatin Kano data tabbatar mana da Makarantar lafiyar mu. - Tambai Ƙwa.

 Muna kira da Gwamnatin Kano data tabbatar mana da Makarantar lafiyar mu. - Tambai Ƙwa.

✍️ Abdul gaffar isah

Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Hon. Alh. Ado Tambai Ƙwa ya buƙaci ya buƙaci Gwamnatin jihar Kano data tabbatar  da makarantar lafiya da akace an kawo ta Dawakin Tofa.


Tambai yayi roƙon ne lokacin da yake jawabin maraba yayin gudanarda taron ƙaddamar da Asibitin ido a cikin babban asibitin Dawakin Tofa.

Yace " Aƙalla sun kai Ɗalibai sama da 500 makarantun lafiya a waje, idan wannan makaranta ta tabbata ba zasu sha wahala ba wajen samar musu da guraben karatu.

Sannan yayi godiya da wannan aiki na ido da aka ƙaddamar a ƙaramar hukumar, kazalika ya yabawa ɗan takarar majalisar tarayya Hon. Abba Ganduje bisa gudunmawarsa a wannan tallafi.

No comments:

Post a Comment