Tuesday, October 18, 2022

An Kusa Daina Karatun Dare Da Itace A Tsangayun Kano Ta Arewa. Shirin Barau.

 Barau Maliya Zai Rabawa Tsangayun Alkur'ani 1,000 Solar Domin Karatun Dare

An Kusa Daina Karatun Dare Da Itace A Tsangayun Kano Ta Arewa. Shirin Barau


.

Daga: Abdul gaffar isah

A kokarin da yake na kyautata tsarin Makarantun tsangayu a yankin Kano ta Arewa, Sanata Barau I Jibrin Wanda akewa lakabi da Maliya, ya kammala shirye shiryen raba Na'urar hasken wutar lantarki Mai aiki da hasken rana a tsangayu 1,000 na yankin da yake wakilta domin daina Karatu da kirare da Kara alokacin karatuttukan almajirai na dare.

Mai taimakawa Sanatan na musamman Alhaji Hashim Sarki (Chairman ) ne ya bayyana haka alokacin taron Alarammomin Majalisar Mahaddata Alkur'ani Na Jihar Kano masu goyon bayan Takarar ta Barau Jibrin da Dakta Nasiru Yusif Gawuna da Mataimakinsa Murtala Sule Garo da sauran 'yan takarkarun Jam'iyyar APC daga sama har kasa Wanda aka gudanar a cibiyar harkokin addinin Musulunci na Karamar Hukumar Kabo cikin makon da ya gabata.

Hashimu Sarki yace babu shakka Mai girma Sanata Barau na sane da kyakkyawar Alaka Tsakaninsa da Alarammomi Mahaddata Alkur'ani, hakan ce ma tasa yanzu Haka Wakilin al'ummar Kano ta Arewa a Majalisar dattijai ta Kasa Rt. Hon. Barau I. Jibrin ya kammala Shirin rabon Solar ga tsangayu 1,000 na yankin Kano ta Arewa a wani kakari da yake na saukakawa Alarammomi yadda suke gudanar da karatuttukan da daddare a tsangayunsu.

Hakazalika ya bayyana cewa Tafiyar Barau I Jibrin tafiya ce ta Amana tsakaninsa da Alarammomi ahlullahi, yace ko a 'yan watanni da Suka Gabata Sanatan ya rabawa alaramomi, dagatai da masu unguwanni takin zamani domin gudanar harkokin Noma, baya ga rabon abubuwan Hawa domin Suma sun amfana da Wakilcin da Suka tura Dan Majalisar dattijan nasu. Kuma yace kowa ya Kara kwantar da hankalinsa, yanzu Sanata Barau ya Fara Saukewa Jama'ar da yake wakilta kabakin arziki.

Akarshe da yake tsokaci Kan Shirin Majalisar Mahaddata Alkur'ani Na yankin Kan shirye shiryen taron addu'ar Saukar Alkur'ani 1,111 Wanda ake fatan gudanarwa, yace ko shakka babu Sanata Barau mutum ne mai Kaunar addu'a domin itace ke zaune da Jihar Kano  lafiya da Kasa Baki Daya, saboda Haka da yardar Allah Idan lokaci yayi a shirye Sanata yake domin bayar da gudunmawa domin gudanar da wannan taron addu'a domin samun dorewar zaman lafiya da Kuma samun nasarar Zaɓen Shekara ta 2023.

Daga nan Hashimu ya godewa Alarammomin bisa goyon baya da addu'o'in da ake Masa a kowane lokaci, sannan yayi fatan Allah ya Maida kowa gidansa lafiya.

Alokacin taron Shugabannin Majalisar Mahaddata Alkur'ani Na Kananan Hukumomin Shiyyar Kano ta Arewa Goma Sha uku duk sun halarci taron da kuma Jagoran Tafiyar APC daga sama har Kasa na Jihar Kano Gwani Laminu Mahmud Salga da sauran 'yan tawagasrsa ne suka halarci wannan gagarumin taro.
©️ Muhammad Abdullahi

No comments:

Post a Comment