Monday, October 17, 2022

Wata kotu ta yankewa wani mutum ɗaurin wata 6 ko tarar dubu 10

 K


utun Shari'ar Muslunci dake zamanta a Dawakin Tofa, daura da Ofishin ƴan-sanda, ta yankewa wani magidanchi Ɗaurin wata shida a gidan gyaran hali ko zaɓin tara na ₦ dubu goma.

Tun da fari magidancin me suna Muhd Bello ɗan kimanin shekaru arba'in an zarge shi da laifin tare wani mutum me suna Abubakar Abubakar tare da raɗe shi da sanda wanda hakan yayi sanadin ji masa rauni, sannan kuma da kalaman tsoratarwa dana ɓatanci.

Me karanto kunshin tuhume-tuhumen yace A dalilin haka Ƙudin Abubakar kimanin ₦ dubu goma sha biyar sun salwanta, haɗin da wayarsa wanda akayiwa kiyasin ₦ dubu takwas, se kuma kudin magani da Abubakar yasha bayan bugeshi da akayi wanda kuɗin su ya kai ₦ dubu biyu da ɗari biyar.

Koda aka karantawa Bello ƙunshin tuhume-tuhumen nan take ya amsa, se dai yace ba hakan nan ya buge Bello ba, biyo shi yayi ze kaɗe shi da babur shi kuma ya buge shi dan ya kare kansa.

Me Shari'a Muhammad Sharif ya tambayi me ƙara ko haka akayi, Nan take Abubakar ya musanta zargin.

Me Shari'a ya ƙara tambayar Bello meya haɗa su wannan rigimar, Muhd Bello yace shi Abubakar ne yayi lalata da matarsa.

Bello ya ƙara da cewa tun kafin su rabu da tsohuwar matartasa Abubakar yake bibiyar ta.

Se dai Abubakar ya musanta wannan zargi.

Me Shari'a ya tashi wani magidanci don yayi ƙarin haske kan lamarin: mutumin ya fara da cewa dama wannan rigimar tasu tsohuwa ce, kuma ita waccan mata da Bello yake magana akan ta yanzu haka matar Abubakar ce, Kuma an ɗaura auren nema agaban hukumar Hisba. Mutumin ya ƙara da cewa Bello ya saki matartasa amma yayi togaciyar cewa banda Abubakar ya sakarwa.

Bello ya yarda da wannan maganar, sedai yace ai duk da haka Abubakar yana bibiyar matartasa tun basu rabu ba.

Me Shari'a ya tambayi Abubakar abinda ya faru, se yace "Bayan Bello ya saki matar tasa ta gama idda shi kuma yaga yana sonta akayi magana sukayi Aure.

A ƙarshe me Shari'a Muhammad Sharif ya yanke hukuncin wata shida ko zaɓin tara ta ₦ dubu goma ga Bello, bisa lefin ɗaukar doka a hannu. Sannan ze biya Ranko na duk abinda aka rasa.

No comments:

Post a Comment