Monday, October 31, 2022

Atiku Abubakar ya taya tawagar Tamaula ta mata murnar samun tagulla.


 Atiku Abubakar ya taya tawagar Tamaula ta mata murnar samun tagulla.

✍️ Abdul gaffar isah

Ɗan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya taya tawagar Flamingoes murnar samun tagulla, a gasar cin kofin duniya na mata.


A wani saƙo daya wallafa a shafin sa na facebook ya bayyana cewar " Ina taya Flamingoes din mu murnar samun lambar tagulla a gasar cin kofin duniya na mata na ƴan ƙasa da 17 a Indiya. 

Ya kuma bayyana cewa " Fiye da mako guda da suka gabata, sun sami cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta mata ta ƴan ƙasa da 17 a karon farko.  Yau kuma sun kawo mana lambar yabo. 

A ƙarshe Atiku ya bayyana matuƙar jin daɗin sa da wannan lambar yabo da suka samu.

No comments:

Post a Comment