Tuesday, November 1, 2022

Dokokin Babban Bankin ƙasa CBN na ƙara saka mutanen arewa a talauci. Sherif Almuhajir.

Dokokin Babban Bankin ƙasa CBN na ƙara saka mutanen arewa a talauci. Sherif Almuhajir.

✍️ Abdul gaffar isah

Shugaban Bankin manoma na jihar Yobe Dr. Sherrif Almuhajir yace Dokokin Babban bankin kasa CBN suna ƙara saka mutanen arewa a cikin tsanani, a lokacin da suke ƙara azurta mutanen kudu.

Almuhajir ya bayyana haka ne ta cikin wani Faifan Bidiyo da ya wallafa a shafin sa na facebook a daren jiya Litinin.

Yace "wasu watanni shida da suka gabata  yayi bayani kan Wasu dokokin CBN da Development Bank of Nigeria da sauran Bankuna yadda yake ganin tsare-tsaren su  suna da tsauri ga ƴan Arewa musamman ma musulmin su, yace "hakan na ƙara tsananta talauci a arewa yayinda yake ƙara azurta mutanen kudu.

Almuhajir yace "Dokokin dai daga nan zuwa shekar 100 babu yadda za'ayi ɗan arewa yaji daɗin tsarin tattalin arzikin Nigeriya muddin idan ba'a duba su ba.

Dr. Sherif dai yace "Tabbas akwai son rai a tsare-tsaren bankin se dai yana kira ga masu Ruwa da tsaki su ƙara duba tsare-tsaren da kyau.

Dayake jawabi Game da canjin kuɗin da ake shirin yi nan ba da daɗewa ba, Dr. Sheriff Almuhajir yayi kira ga CBN daya ƙara lokaci, saboda mutanen arewa dayawa basu saba da mu'amala da banki ba, kuma idan akayi shi kamar yadda aka tsara ze daɗa karya wasu ƴan kasuwar arewacin kasar, ya ƙara da cewa "zaka iya samun wanda yake da miliyan 500 amma kuɗi hannu, yanzu wannan idan kace yaje ya saka su a banki lokaci ɗaya tabbatas hukumar NFIU seta bincike shi, alhali kuma halattattun kudade ne.

Sannan ya bayyana cewar akwai waɗanda su kuma sunyi nisa da Bankin ne shiyasa basama ajiye kuɗin su abanki, ya ƙara da cewa  "A jihar Yobe kananan hukumomi 4 ne suke da bankuna tayaya zakace kowa ya maida kuɗi banki bayan har yanzu wasu basu sanshi ba.

Daga cikin abubuwan da masanin ya bayyana waɗanda ke ƙara karya tattalin arzikin Arewa " Development Bank of Nigeria banki ne da akayi shi dan ƴan Nigeriya, yace "A shekarar data gabata sun raba kuɗi ₦ biliyan 400 da 82 a Nigeriya, amma kaso Hamsin da bakwai an kaisu south/west na kudancin Nageriya ɓangaren yarabawa, yayin aka kai kaso goma sha takwas south/south se kuma kaso tara an kaishi south/East.

Dr. Sherrif yace daya haɗa lissafin kudin se yaga an kai biliyan 400 gaba ɗaya kudancin kasar, kuma yace suma ƴan Arewa suna zuwa nema domin shi kansa yace yaje dan karɓowa Jihar Yobe, amma an saka musu dokoki masu tsauri waɗanda ba zasu ciku ba, se dai ya bawa mutani yobe haƙurin cewa baza su samu ba.

Amma gaba ɗaya North/East na arewacin Najeriya kaso ɗaya kawai suka samu a cikin 100, wanda adadin nasa yakai ₦ biliyan 4 da 820, yayinda sukuma North/west a Arewacin kasar suka samu kaso biyar wanda adadin yakai ₦ biliyan 24 da miliyan 100.

Yace Tabbas akwai kuskure da son rai cikin wannan tsari gaba ɗaya arewa basu wuce kaso bakwai ba yayinda Lagos ita kaɗai ta samu ₦ biliyan 247.

Yace dole a canja Dokokin tsarin bankin ta yadda zasu yi daidai da addinin mu, mu'amalar mu, tsarin mu, dakuma yadda zamu iya. bankunan nan da ake assasawa  kudaɗen ƴan Najeriya ne aciki, se dai yayi wani zargin cewa idan an zuba kuɗaɗen ana zagayewa aturawa ƴan kudu suyi kasuwanci dasu.

No comments:

Post a Comment