Wednesday, October 26, 2022

CBN na shirin kaddamar da sabon katin biyan kuɗi na bai-ɗaya a NajeriyaBanki

CBN na shirin kaddamar da sabon katin biyan kuɗi na bai-ɗaya a Najeriya
Banki

✍️ Abdul gaffar isah

Babban bankin Najeriya CBN ya ce zai ƙaddamar da tsarin katin bai-ɗaya ranar 16 ga watan Janairun 2023.

Za a kaddamar da shirin ne karkashin tsarin yarjejeniyoyi tsakanin bankunan kasar (NIBSS) tare da hadin gwiwwa da kwamitin ma'aikatan banki.

A wata sanarwa da kakakin babban bankin kasar Osita Nwanisobi, ya fitar wanda jaridaun Najeriya suka wallafa, ya ce tsarin zai saukaka kashe kudi tare da rage yawan kudin da ake cazar kwastomomi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ''Najeriya ce kasar ta tafi kowacce karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, da kuma ci gaba a fannin fasahar zamanantar da abubuwa, kuma a kokarin babban bankin kasar na bunkasa fannin fasahar zamani ne ya sa ya kirkiro da wannan sabuwar fasaha''.

Babban bankin ya ce baya ga bunkasa fasahar zamani a fannin kasuwancin kasar, shirin zai bayar da dama ga bankunan kasar su warware tarin matsalolin da ke musu dabaibayi.

Idan aka kaddamar da shirin Najeriya za ta bi sahun kasashe irin su Indiya da Turkiya da China da Brazil wadanda suka daɗe suna amfani da tsarin katin biyan kuɗi na bai-ɗaya, kamar yadda babban bankin kasar ya bayyana.
- BBC Hausa

No comments:

Post a Comment