Tuesday, October 25, 2022

An raba takardun shiga makarantun lafiya a Dawaki.

An raba takardun shiga makarantun lafiya a Dawaki.


✍️ Abdul gaffar isah


Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Alh Ado Tambai Kwa ya jagoranci raba takardun Admission ga Ɗaliban lafiya ƴan-Ƙaramar Hukumar.



An raba takardun shaidar daukar daliban ne ga kimanin mutam 50 a makarantun Bichi Academy, da kuma school of Health sciences and technology Kazaure.


Idan baku manta ba abaya mun kawo muku shiri kai tsaye kan yadda shugaban yake raba takardun ɗaukar aiki da kuma bayar da Takardun shiga makarantun gaba da sikandare.


Mun tuntuɓi me kula da wannan ɓangare, ya kuma sheda mana cewa " akwai ɗalibai daza'a cigaba da turawa karatu kyauta nan gaba.


Taron ya samu halartar manyan mutane kama daga shi kansa shugaban ƙaramar hukumar da kuma matemakin sa Alh. Garba lebo da wakilin Hakimi Alh. Kabiru Aliyu da kasiloli da kuma masu bada shawara na musamman.


No comments:

Post a Comment