Thursday, October 27, 2022

Ganduje ya buɗe asibitin Ido a Dawaki.

 Ganduje ya buɗe asibitin Ido a Dawaki


✍️ Abdul gaffar isah

Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya buɗe asibitin Ido a Dawakin Tofa.

Gwamna Ganduje ya buɗe asibitin ne da yammacin wannan rana ta Alhamis a Babban Asibitin ƙaramar hukumar dake cikin garin Dawaki, da tallafin Ɗan takarar majalisar tarayya a Dawakin Tofa, Tofa, R/ Gado.

Ajawabin Gwamnan lokacin ƙaddamar da buɗe wannan asibiti yace "sunyi amfani da wannan rana ne wadda majalisar dinkin duniya ta ware kan bikin kula da masu larurar ido, domin yin ayyuka guda uku.

1. Buɗe wannan Asibitin na ido wanda yake acikin Babban Asibitin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.
2. Aikin Haƙora ga masu ɗauke da larurorin haƙori kyauta.
3. Ƙaddamar da kwamitin daze riƙa kula da wannan asibiti.

Shima anasa jawabin me martaba sarkin Bichi Alh. Nasiru Ado Bayero yabawa Gwamnatin Kano bisa wannan gagarumin aiki, ya kuma yi kira ga al'umma dasu riƙa bin shawarwarin likitoci musamman bangaren daya shafi Ido.

Kwamishinan lafiya na jahar Kano Dr Tsanyawa shima ya yabawa Gwamnan Kano ya kuma bayyana cewa sama da mutane 4000 ne zasu ci gajiyar wannan aiki na Ido da Haƙora kyauta. A mazaɓun Dawakin Tofa, Tofa, R/Gado.

No comments:

Post a Comment