Friday, October 28, 2022

Sarkin Bichi yace wajibi ne mutane su riƙa kula da Lafiyar su.

 Sarkin Bichi yace wajibi ne mutane su riƙa kula da Lafiyar su.

✍️ Abdul gaffar isah

Mai martaba sarkin Bichi Alh Dr. Nasiru Ado Bayero yace " Dole mutane su kula da lafiyar su, musanman lafiyar idanu.


Hakan ne zuwa ne lokacin da yake mika jawabin sa yayin ƙaddamar da Asibitin ido wanda aka buɗe a Dawakin Tofa.

Mai martaban ya yabawa Gwamnatin jihar Kano bisa haɗa taron gangamin dan tallafawa masu larurar ido saboda inganta lafiyar al'umma.

Sarkin yayi kira ga al'umma dasu riƙa bin shawarwarin likitoci, su kuma riƙa zuwa ana duba lafiyar su, dan kaucewa makanta, ya ƙara da cewa suma masu hawan jini da ciwon suga su kula sosai saboda wani lokacin suna da alaƙa da kawo ciwon makanta.

Kazalika yayi kira da cewar " Ariƙa kula da tsaftace jiki da muhalli, akuma riƙa zuwa asibiti akan lokaci.

A ƙarshe ya rufe jawabin nasa da Addu'ar zaman lafiya, da ƙaruwar arziki da wadata.

No comments:

Post a Comment