Sunday, October 16, 2022

Ina tausayawa duk shugaban da zezo. - sunusi.

 


Kar ku zaɓi duk ɗan takarar da ya ce gyaran Najeriya abu ne mai sauƙi - Sanusi

Muhammadu Sanusi ya ce "dole ne sai an shiga mawuyacin hali" kafin a gyara Najeriya

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Muhammadu Sanusi II ya gargaɗi 'yan ƙasar cewa gyaran Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba, yana mai cewa duk ɗan takarar da ya faɗi akasin haka "ƙarya yake yi".

Kazalika Sanusi, wanda sarkin Kano ne mai murabus, ya shawarci masu jefa ƙuri'a da kar su zaɓi duk ɗan siyasar da ya ce gyaran Najeriya abu ne mai sauƙi.

"Matakan da za a ɗauka na gyara wannan [Najeriya] ba za su yi daɗi ba," in ji shi yayin da yake magana a taron zuba jari da gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya ranar Asabar.

Taron ya samu halartar manyan baƙi kamar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC mai mulki, da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru, da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu da sauransu.

Haka nan, Ƙaramar Ministar Kasuwanci Mariam Yalwaji Katagum ce ta wakilci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a wurin taron da ake kira KadInvest, wanda ake gudanarwa shekara-shekara karo na bakwai - 7.0.

'Ko dai ƙarya yake yi muku ko kuma bai san aikin ba'

Muhammadu Sanusi ne mataimakin shugaban hukumar zuba jari ta Kaduna

Sanusi Lamido Sanusi - wanda a yanzu ake kira Muhammadu Sanusi - shi ne mataimakin shugaban hukumar zuba jari ta Kaduna mai suna Kaduna Investment Promotion Agency.

Da yake gabatar da jawabinsa, tsohon gwamnan na CBN ya ce ganin yadda ake samun raguwa a kuɗaɗen haraji da kuma ɗumbin bashin da ake bin Najeriya, wajibi ne a ɗauki "matakai masu tsauri".

"Matakan da za a ɗauka dole ne su zama masu tsauri. Saboda haka bari na shawarci 'yan siyasarmu, dole ne ku faɗa wa 'yan Najeriya gaskiya game da mawuyacin halin da za a shiga.

"Duk wanda ya faɗa muku cewa cikin sauƙi za a yi gyara kar ku zaɓe shi, saboda ko dai ƙarya yake yi muku ko kuma bai san irin aikin da ke gabansa ba."

Sarkin na Kano mai murabus yana ganin cewa lallai sai an gyara tsarin biyan kuɗin lantarki da farashin man fetur, yana mai cewa "ana zuzuta yawan man da 'yan Najeriya ke sha a kullum".

A cewarsa: "Wajibi ne sai an ɗauki matakan da suka dace. Amma kafin a yi hakan, dole sai an gyara adadi na ƙarya da ake bayyanawa, sai an yaƙi cin hanci."

Abin da sabon shugaban ƙasa ya kamata ya fara yi
Da ma an san Sanusi da ra'ayin goyon bayan cire tallafin man fetur, wanda bai gushe ba sai da ya yi kira ga duk wanda ya yi nasarar zama shugaban ƙasa a 2023 da ya yi bincike a ɓangaren tallafin.

Ya ce: "Ina fatan duk wanda ya zama shugaban ƙasa a 2023, abin da zai fara yi shi ne ya nemi kamfanin mai na NNPC ya yi bayani kan duk dalar da ya karɓa a matsayin kuɗin tallafin mai.

"Dole ne su ba da bayanan jiragen ruwan da suka shigo wanda kuma za a iya tabbatarwa daga kamfanonin inshora ko da gaske ne jirgin ya sauka a Najeriya a wannan ranar.

"Saboda doka ta ce dole ne sai an nuna hujja kafin a karɓi kuɗin tallafi kuma dole ne sai an ba da hujja cewa an kawo man a kan farashin da mutum ya ce ya kawo shi. Haka doka ta ce."

Tuni gwamnatin Buhari ta ce ta shirya daina biyan tallafin daga tsakiyar shekarar 2023, daidai lokacin da zai bar mulki bayan ya shafe wa'adi biyu na shekara takwas jimilla.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnati na kashe fiye da naira tiriliyan ɗaya duk wata wajen biyan tallafin fetur, abin da masana tattalin arziki irin su Muhammadu Sanusi ke cewa gara a karkatar da su kan ayyukan raya ƙasa.

No comments:

Post a Comment