Monday, October 17, 2022

Ƴan-sanda sun kafa gidauniyar tallafawa marayu.

 J







ami'an Ƴan sandan Dawakin Tofa sun  gidauniyar tallafawa marayu waɗanda iyayen su suka rasu suna bakin aiki.

Ƴan sandan sun kafa wannan gidauniya ne biyo bayan tarin marayu da ake dasu, waɗanda iyayen su ƴan sanda ne.

Ayayin taron ƙaddamar da gidauniyar wanda akayi a jiya acikin makarantar Firamare dake karamar hukumar Dawakin Tofa, ɗaukacin jami'an sun fito don nuna goyon bayansu.

A jawabin da matemakin shugaban gidauniyar ASP Usman Ubale Ukashatu yayi man ya bayyana cewar " wannan shine aikin daya dace suyi dan tallafawa ƴaƴan abokan aikin su.

Anasa jawabin ma'ajin gidauniyar DSP Alhaji Ashhabu yace "suna cire wani abu ne cikin Albashin su dan tallafawa ƴaƴan su, ya ƙara da cewa suna tunanin yadda zasu faɗaɗa gidauniyar zuwa ga kowa da kowa.

Wannan dai shine karo na farko da aka samu wasu ma'aikata da suka gina irin wannan gidauniya dan tallafawa ƴa ƴan abokan aikin su.

Aƙarshe jami'an sunyi kira ga sauran ma'aikata da suyi koyi da wannan aiki.
>.

No comments:

Post a Comment