Friday, November 4, 2022

Ilimi ya samu kaso mafi tsoka a cikin kudirin kasafin kudi na N245bn na Ganduje na karshe.


Ilimi ya samu kaso mafi tsoka a cikin kudirin kasafin kudi na N245bn na Ganduje na karshe.

✍️ Abdul gaffar isah

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya gabatar da kudurin kasafin kudi na shekarar 2023 na naira biliyan 245 wanda bangaren ilimi ya samu kaso mafi tsoka.


Gwamnan jihar Kano,  Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da kasafin kudi na Naira biliyan 245 na shekarar 2023 ga majalisar dokokin jihar domin amincewa.

Da ya ke gabatar da kasafin a yau Juma’a a Kano, Ganduje ya ce an sanya wa kasafin kuɗin, mai taken kasafi na ci-gaba da  wadata II, da nufin karfafawa tare da inganta rayuwar al’ummar jihar.

Ya ce kasafin ya kunshi manyan ayyuka  da za a kashe Naira biliyan 144, wanda ya nuna kashi 59 cikin 100 da kuma Naira biliyan 100 da za a kashe a harkokin yau da kullum, wanda ya nuna kashi 41 cikin 100.

Gwamnan ya ce bangaren ilimi shi ne ya fi ɗaukar kaso mafi tsoka, inda a ka ware masa Naira biliyan 62, wanda ya nuna kashi 27 cikin 100 fiye da adadin da UNESCO da Majalisar Dinkin Duniya suka ba da shawarar a rika fitar wa, inda ya ce za a fitar da kudaden ne wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsare da nufin tabbatar da ingantaccen ilimi a dukkan matakai.

Ya ce za a kuma yi amfani da wani bangare na kudaden wajen inganta shirin ilimi kyauta kuma dole a jihar.

Ganduje ya ce an ware wa fannin lafiya Naira biliyan 39.1, albarkatun ruwa Naira biliyan 15, ɓangaren sufuri Naira biliyan 8.6, fannin noma Naira biliyan 19.9 da ayyuka da kayayyakin more rayuwa Naira biliyan 35.

Ya bukaci ‘yan majalisar su tabbatar da  gaggauta amincewa da kasafin kudin domin baiwa gwamnati damar ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar.

Gwamnan ya kuma bukaci matasa da su guji duk wani tashin hankali musamman ganin zaben 2023 ya kara kusanto.

A nasa jawabin shugaban majalisar, Alhaji Hamisu Chidari, ya baiwa gwamnan tabbacin yin gaggawar zartar da kasafin kudin domin samun damar darewa kan kasafin kudin watan Janairu zuwa Disamba.

Chidari ya bukaci Ma'aikatun Gwamnati da Hukumomi (MDAs) da su kasance a shirye don kare kasafin kudi a majalisar.

Kakakin majalisar ya kuma yaba wa gwamnan bisa kokarin da ya ke yi a bangaren samar da ababen more rayuwa, tsaro, lafiya da ilimi.


No comments:

Post a Comment