Thursday, November 10, 2022

Naira tana farfaɗowa, bayan doguwar tazarar da aka bata.

 Darajar naira ta ƙaru da kashi 16.6% idan aka kwatanta da dalar Amurka a cikin kwana uku


.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ce an sayar da dalar Amurka ɗaya kan Naira 765 a kasuwar bayan fage a yammacin Alhamis.

Hakan na zuwa ne bayan da kasuwa ta buɗe ana sayar da nairar a kan 800 kan dala guda.

Masu hada-hadar kuɗi sun ce hakan ya faru ne sanadiyyar yadda aka rage neman dalar a kasuwa.

Haka nan kuma an fara samun wadatuwar dalar a kasuwar.

A makon da ya gabata dai, masu sana’ar canji a Najeriyar sun ce al’umma sun rinƙa turuwa zuwa wuraren canjin kuɗi bayan da babban bankin Najeriya ya bayar da sanarwar sauya wasu daga cikin takardun kuɗin ƙasar.

Darajar naira dai ta rinƙa faɗuwa a kasuwar bayan fage tun farkon 2022.

An dai rinƙa samun banbanci mai yawa tsakanin farashin dalar a hukumance da kuma na kasuwannin bayan fage.

Inda a hukumance farashin dalar ya kasance tsakanin naira 410 zuwa 450.

No comments:

Post a Comment