Friday, November 11, 2022

Ya kamata a rage Albashin ƴan-majilisa dan biyan malaman jami'o'i. "Ndume

 S


anata Ali Ndume ya shawarci Gwamnatin tarayya ta zabtare Albashin ƴan majalisa da kashi 50 cikin 100 domin biyan malaman jami'o'i dake yajin aiki kuɗaɗen su.

Sanata Ndume dake wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattijai ya shaida haka ne a lokacin wani taro daya gudana a birnin Maidugurin.

Ya ƙara da cewa wannan abu ne daya shafi ƙasa baki ɗaya kuma dole a wasu lokutan a ɗau matakan ceto ƴan ƙasa da ilimi.

Kiran da Sanatan yayi na zuwa ne daidai lokacin da malaman jami'o'i ke ƙorafin cewa rabin Albashin su aka basu bayan sun janye yajin aikin.

Ɗan majalisar dai yace " lokaci yayi da Yakamata a shawo kan matsalolin dake durƙusar da fannin ilimi a Nigeriya.

A watan Oktoban daya gabata ne, ASUU ta janye yajin aikin data shafe wata takwas tana yi batare da biyan buƙatun ta daga wajen Gwamnatin tarayya ba.

No comments:

Post a Comment