Tuesday, October 25, 2022

Ɗalibai 29 sun sauke Alqur'ani

 Ɗalibai 29 sun sauke Alqur'ani

✍️ Abdul gaffar isah

Makarantar munawwara islamiyya dake ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta yaye ɗalibai 29 da suka kammala saukar Alqur'ani mai girma.


Munawwara islamiyya ta kasance farkon islamiyya a Dawakin Tofa, tanada tsohon tarihi mai ban sha'awa, ta kuma yaye mahaddata da dama.

Ajiya Lahadi makarantar ta yaye dalibai 29 waɗanda suka sauke Alqur'ani mai girma 25 daga cikin su mata ne yayinda 4n suka kasance maza.

A jawabin malamin Qur'anin nasu mal. Ayuba saminu yace "sun fara karatun ne da kusan mutum 60, amma sun kammala da mutane 29, duk da wasu daga cikin ɗaliban sunyi aure.

Shima anasa jawabin mal. Mukhtar Usman yace "sunyi aiki tuƙuru da ɗaliban, kuma babu wani lokaci da ba'a cikin karatu suke ba, tun daga safe, rana, dare.

Shugaban makarantar mal. Musa Muhammad ya nuna matukar farin cikin sa ga wannan sauka.

Suma iyayen yara sun nuna farin cikin su sosai, sun kuma yi godiya ga malaman da suka tsaya kai da fata har ƴaƴan su suka sami wannan karatu.

Suma waɗanda sukayi saukar sun nuna farin cikinsu dakuma godiyar su ga malaman su jajirtattu.

Taron walimar ya samu halartar manyan mutane ciki harda wakilin Hakimin Dawakin Tofa Alh. Kabiru Aliyu.

No comments:

Post a Comment