Tuesday, October 25, 2022

Wani ɗan ƙasar Malawi ya rushe gidan da ya ginawa matar sa da mahaifiyar ta bayan da wani mutum ya kasa shi.

 Wani ɗan ƙasar Malawi ya rushe gidan da ya ginawa matar sa da mahaifiyar ta bayan da wani mutum ya kasa shi.




✍️ Abdul gaffar isah


Mutumin ɗan ƙasar Malawi me suna farancis Bonda ya rushe gidan ne bayan wani mutumin daban ya kasa shi.


Awani Faifan Bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta Banda yace "tsawon shekaru 13 suna tare da matar tasa kuma sunada ƴaƴa uku.


Alokacin auren nasu Banda yayi ƙoƙarin gina gidaje guda biyu ɗaya na matar tasa ɗaya kuma na mahaifiyar ta.


A cewar Banda matar tashi ta fara soyayya da wani mutumin kuma yanzu haka ma ta bar gida.


Banda yayi ƙoƙarin tuntuɓarta se dai koyaushe wayarta na cikin amsa kira ga shi sanon saurayin nata.


Wannanne yasa Banda ya ɗauki wannan mataki na rushe gidajen biyu Na matar dana mahaifiyar Tata.

No comments:

Post a Comment