Friday, October 28, 2022

Kwankwaso Zai Kawo Sama Da Kuri'a Miliyan 50 Arewa A Cewar Buba Galadima.

Kwankwaso Zai Kawo Sama Da Kuri'a Miliyan 50 Arewa A Cewar Buba Galadima. 

✍️ Abdul gaffar isah

Tsohon mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar APC, Injiniya Buba Galadima, ya ce Kwankwaso ne zai lashe zabe a dukkan jihohin arewa 19 a zaben shugabancin kasa na 2023 dake zuwa. 

Cikin wata  tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV, a jiya Alhamis, Nuna Galadima yace Kwankwaso zai lashe zabe a shiyoyi uku na arewa kuma ya samu kuri’u a inda abokan hamayyarsa ke da karfi. 

PDP bata kan takardar kada kuri’a saboda karfin ta a kudu maso gabas ne wanda kuma Peter Obi suke yi.

 Wurin da PDP ke da karfi kuma shi ne kudu maso kudu. Kamar yadda Wike baya goyon bayan Atiku, kudu maso kudu ta kubuce masa.” 

Buba Galadima yace Arewa dukkanta ta Kwankwaso ce saboda zai kawo Taraba, Adamawa, Gombe da Bauchi wanda ya hada da gwamnoninsu. 

“Zai yi nasara a arewa maso gabas, arewa ta tsakiya kuma ya kawo arewa maso yamma. Idan aka hada duka, zasu samu kuri’u sama da miliyan hamsin. 

Kwankwaso zai samu wani kaso a kudu maso kudu, kudu maso gabas da kudu maso yamma. 

Saboda haka inada tabbacin kada da daɗa, kada ka rage Kwankwaso ne zai lashe zaben shugaban kasa a cewar Buba Galadima.

No comments:

Post a Comment