Friday, October 28, 2022

Mun yiwa kanawa kyakkyawan tanadi. - Sunusi Bature.



Mun yiwa kanawa kyakkyawan tanadi. - Sunusi Bature

✍️ Abdul gaffar isah

Me magana da yawun Ɗan takarar Gwamnan jihar Kano Abba gida-gida a jam'iyyar NNPP sunusi Bature Dawakin-Tofa yace " Akwai kyakkyawan Tanadi da Abban ya shiryawa kanawa, wanda za'a bayyana nan ba da daɗewa ba.

Sunusi ya bayyana haka ne ta cikin wani jawabi da ya yiwa manema labarai, game da rashin halartar Abba gida-gida wani taron da aka shiryawa ƴan takara.

Sunusi dai ya bayyana cewar "Dr. Abubakar Yusuf labaran ya wakilci Ɗan takarar a wancan taro se dai tunda bashine ɗan takara ba  bazai sami damar shiga ba.

Se dai kakakin jam'iyyar NNPP ɗin Sunusi Bature yace duk da haka suna da ƙudure-ƙudure masu kyau a harkar lafiya, Noma, ilimi da sauran al'amuran rayuwa. Wanda yace nan bada daɗewa ba Ɗan takarar su Abba gida-gida ze ƙaddamar dasu a bainar jama'a.

No comments:

Post a Comment